Sojoji Sun Sauya Taku, An Tura Zazzafan Gargadi ga 'Yan Ta'adda
- Rundunar Sojin Najeriya ta ce ta sauya tsarin tsaro a Kebbe da garuruwan da ke makwabtaka da yankin bayan samun bayanan sirri
- An gano cewa ‘yan ta’addan da suka kai hari a kashen makon da ya gabata har yanzu suna kusa da yankin kuma za a dana masu tarko
- Babban Kwamandan Runduna ta 8, Manjo Janar Bemgha Koughna, ya gana da shugabannin al’umma tare da duba halin tsaro a Kebbe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Sokoto – Rundunar Sojin Najeriya ta sauya tsarin tsaro a Karamar Hukumar Kebbe ta Jihar Sokoto da yankunan da ke makwabtaka da ita.
Wannan ya biyo bayan harin da aka kai a ranar Juma’a da kuma samun bayanan sirri cewa ‘yan ta’addan da suka kai harin har yanzu suna kusa da yankin.

Source: Facebook
Premium Times matakin ya biyo bayan ziyarar duba ayyukan tsaro da Babban Kwamandan Runduna ta 8, Manjo Janar Bemgha Koughna, ya kai sansanin soji na gaba da ke Kebbe da sauran al’ummomin da ke kewaye da yankin a ranar Lahadi, 16 ga watan Agusta, 2026.
An samu labarin hari a Sokoto
Jaridar Punch ta wallafa cewa da farko, rundunar ta ce ziyarar ta biyo bayan rahotannin wani “sabon hari” da aka kai wa al’ummar Ungushi da ke Kebbe a Sokoto.
Sai dai Laftanar Kanal Olaniyi Osoba, Mukaddashin Mataimakin Daraktan Hulɗa da Jama’a na Runduna ta 8 da Sashi na Biyu na 'operation Fansam Yamma' , ya bayyana cewa rundunar ta samu bayanan sirri ne da ke nuna cewa ‘yan ta’addan har yanzu suna kusa da yankin.
Ya ce:
“An samu rahoton sirri cewa ‘yan ta’addan har yanzu suna kusa.
An tsaurara tsaro a Sokoto
Rundunar ta ce bayan samun bayanan, Manjo Janar Koughna ya sake tsara tsarin tsaron yankin domin hana ‘yan ta’adda sake kutsawa cikin al’ummomin da kuma kara kare wuraren da ke cikin hadari a kan hanyar Sokoto zuwa Kebbi.
A yayin ziyarar, kwamandan ya gana da shugabannin al’umma da mazauna yankin domin tantance halin tsaro da kuma jin koke-kokensu.
Rundunar ta ce Koughna ya tabbatar wa mazauna yankin cewa sojoji na ci gaba da kasancewa a wuraren da aka tura su tare da kasancewa cikin shirin ko-ta-kwana domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
Ya bukaci mazauna yankin da su kwantar da hankalinsu, su ci gaba da gudanar da harkokinsu na halal tare da bayar da hadin kai ga jami’an tsaro.
An kai hari jihar Sokoto
A baya, kun ji cewa akalla mutane 32 ne aka kashe a wani hari da ake zargin ’yan bindiga ne suka kai a garin Ungushi da ke ƙaramar hukumar Kebbe ta Jihar Sokoto da ke Arewa maso Yamma.
Mazauna yankin sun ce maharan sun shafe tsawon lokaci suna kai hari, inda suka kuma kashe wasu daga cikin mutanen da suka yi ƙoƙarin kare garin
Wani jagoran garin da ya shaida harin kuma ya halarci jana’izar wasu daga cikin waɗanda aka kashe ya bayyana hakan, yana mai cewa ’yan bindigar sun mamaye garin Read more:
Asali: Legit.ng

