Juyin Mulki: Abin da Ya Hana IBB Ceton Ran Abokinsa, Mamman Vatsa
- Tsohon shugaban mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babangida, ya bayyana cewa ba da gangan ya ki ceton ran abokinsa, Janar Mamman Vatsa
- Vatsa na daga cikin sojojin da aka ce an kama da laifin kitsa juyin mulki, daga baya aka yanke masa hukuncin kisa ta hanyar harbi tare da wadanda aka kama da laifin
- Da ya ke karin bayani game da yadda ya zura ido aka harbe Vatsa a watan Maris na 1986, Ibrahim Badamasi Babangida ya yi mamakin hannunsa a juyin mulki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. Jihar Niger – Tsohon shugaban mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, wanda aka fi sani da IBB, ya bayyana dalilin da ya sa ya kasa hana kashe babban abokinsa kuma abokin aikinsa, Janar Mamman Vatsa.
Wasu sojoji sun kaddamar wa Janar Vatsa da sauran wadana aka kama da hukuncikisa bayan an same su da hannu a zargin yunkurin juyin mulki a shekarar 1985.

Source: Twitter
Nigerian Tribune ta kawo labarin cewa Ibrahim Badamasi Babangida ya bayyana hakan ne a Minna, jihar Neja, yayin shirye-shiryen bikin cikar sa shekaru 85 da haihuwa.
Dalilin IBB na nade hannu kan Vatsa
A ruwayar Daily Post, lokacin da lamarin ya faru, Vatsa shi ne Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), kuma an zarge shi da hannu a wani shirin hambarar da gwamnatin Babangida.
Da yake tunawa da abin da ya faru, Babangida ya ce da farko ya yi 'ki ya yarda da rahotannin da ke alakanta Vatsa da yunkurin juyin mulki saboda irin kusancin da ke tsakaninsu.
Ya ce:
“Da farko, na kasa yarda da rahotannin da ke alakanta Vatsa da wani shirin juyin mulki saboda dadewar abotarmu da kuma tarihin da muka yi tare.”
Babangida ya ce bayan wani babban jami’in soja ya sanar da shi cewa an ambaci sunayen Vatsa da Mohammed Gado Nasko cikin wadanda ake zargi da hannu a shirin, ya gayyace su zuwa ofishinsa.

Kara karanta wannan
Tsautsayi ya faɗa kan matar aure da 'ya'yanta 2 cikin dare, Allah ya musu rasuwa a Kaduna
Ya kara da cewa:
“Lokacin da suka zo, na tambaye su game da rahotannin cewa an ambaci sunayensu cikin wani shiri na hambarar da gwamnatina. Dukansu sun musanta hannu a ciki."
Yadda aka kama Vatsa da laifi
Daga bisani, an kafa kwamitin binciken soji domin gudanar da bincike kan zargin inda kwamitin ya wanke Janar Gado Nasko daga zargin, amma ya gano wasu shaidu da suka alakanta Vatsa da shirin juyin mulkin.
Tsohon shugaban mulkin sojan ya ce sakamakon binciken ya ba shi mamaki sosai, tare da jefa shi cikin tsananin bakin ciki da takaici. Sai dai ya ce ba shi da ikon shiga tsakani domin dokar soja ce ta tsara hukuncin.

Source: Getty Images
A kalaman IBB:
“Babu abin da zan iya yi domin kubutar da shi daga sakamakon da dokar soja ta tanada. Abin ya fi karfi na. Haka na rasa dan uwana, Janar Mamman Vatsa."
Daga bisani, an kashe Vatsa ta hanyar harbe shi a watan Maris na 1986. Babangida da Vatsa sun dade da sanin juna. Sun girma tare, sun yi karatu a Bida Middle School, wadda yanzu ake kira Government College Bida, sun kammala a shekara guda, sannan daga bisani suka shiga aikin soja tare.
IBB ya fadi masu hannu a juyin mulki
A baya, kun samu labarin cewa tsohon shugaban mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babangida, ya yi magana game da yadda ake yin nasara a duk wani shirin hambarar da gwamnati mai ci ta hanyar juyin mulki.
IBB ya ce attajirai sun taka muhimmiyar rawa wajen tallafawa da daukar nauyin juyin mulkin soja a lokuta daban-daban cikin tarihin Najeriya domin a hambarar da shugaban da ke kan mulki a kawo wani.
Ya kuma bayyana yadda aka samu zargin Mamman Vatsa da hannu cikin yunkurin juyin mulkin shekarar 1985, inda ya bayyana matukar kaduwa da mamakin cewa akwai hannun abokinsa a lamarin.
Asali: Legit.ng

