A karshe, sojojin Najeriya sun kwace kauyen Bula Shatana, 'yan Boko Haram sun mika wuya

A karshe, sojojin Najeriya sun kwace kauyen Bula Shatana, 'yan Boko Haram sun mika wuya

A cigaba da ragargazar mayakan kungiyar Boko Haram da dakarun rundunar sojin Najeriya ke yi, wasu mayakan kungiyar da suka fito daga Bula Bello da Yerima Gana sun mika wuya ga rundunar soji ta 21SAB da ke Bama.

Mayakan, da aka mikasu sashen bincike na musamman a rundunar soji ta 21SAB, sun bayyana cewa sun mika wuya ne sakamakon ruwan wuta da dakarun soji ke yi musu ta sama da kasa.

A wani atisaye da kwamandan rundunar 21SAB ya jagoranta, dakarun soji sun kwace kauyen Bula Shatane daga hannun mayakan kungiyar Boko Haram tare da lalata gidajen karan da suka yi a kauyen.

Manjo Janar John Enenche, shugaban sashen yada labarai na rundunar soji, ya ce mayakan kungiyar Boko Haram sun tsere bayan sun hangi tawagar rundunar sojoji ta nufo kauyen cikin shirin yaki.

Janar Enenche ya ce yanzu haka babu sauran dan kungiyar Boko Haram a kauyen, sannan babu sauran wani abu nasu da ya rage a kauyen.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Janar Enenche ya fitar ranar Alhamis, 29 ga watan Afrilu, 2020.

A karshe, sojojin Najeriya sun kwace kauyen Bula Shatana, 'yan Boko Haram sun mika wuya
A karshe, sojojin Najeriya sun kwace kauyen Bula Shatana, 'yan Boko Haram sun mika wuya
Asali: Twitter

A wata sanarwa da hedikwatar rundunar soji ta fitar, ta ce Jiragen yakin sojojin rundunar atisayen 'Ofireshon Lafiya Dole' sun kashe wasu shugabannin kungiyar Boko Haram yayin da suke wani taro a Kolloram, jihar Borno.

A sanarwar da hedikwatar rundunar tsaro (DHQ) ta fitar, ta bayyana cewa an kaiwa shugannin kungiyar harin ne bayan samun sahihan bayanai a kan taron da suka shirya domin tsara kai wasu hare-hare.

DUBA WANNAN: Annobar covid-19 ta sake hallaka mutane uku a Maiduguri

Sashen watsa labarai na rundunar sojin Najeriya ya fitar da sanarwar cewa an yi wa mayakan kungiyar Boko Haram luguden bama - bamai a ranar Asabar.

Sanarwar ta bayyana cewa rundunar soji za ta cigaba da kai zafafan hare - hare a mafaka da wuraren haduwar mayakan kungiyar Boko Haram da na ISWAP a gefen tekun Chadi.

A cikin sanarwar, manjo janar John Enenche ya ce, "dakarun soji za su cigaba da kai hare - hare a kan 'yan ta'adda a yankin arewa maso gabas.

"A cigaba da kai irin wadannan hare - hare ne rundunar soji ta kaddamar da wani babban hari da jiragenta na yaki a kan 'yan ta'addan kungiyar Boko Haram da ISWAP a Kolloram.

"Mayakan kungiyoyin da dama sun mutu sakamakon ruwan wuta da bama - baman da sojoji suka sakar musu."

A ranar 20 ga watan Afrilu ne rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta sun kashe mayakan kungiyar Boko Haram fiye da 100 a kauyen Buni Gari da ke karkashin karamar hukumar Gujba a jihar Yobe.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng