'Yan Bindiga Sun Yi Ta'addanci a Sokoto, Sun Kashe Mutum 32
- Akalla mutane 32 ne aka kashe a wani hari da ake zargin ’yan bindiga ne suka kai a garin Ungushi da ke ƙaramar hukumar Kebbe ta Jihar Sokoto
- Mazauna yankin sun ce maharan sun shafe tsawon lokaci suna kai hari, inda suka kuma kashe wasu daga cikin mutanen da suka yi ƙoƙarin kare garin
- Wani jagoran garin da ya shaida harin kuma ya halarci jana’izar wasu daga cikin waɗanda aka kashe ya bayyana hakan, yana mai cewa ’yan bindigar sun mamaye garin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Sokoto - Rahotanni sun nuna cewa wasu tarin 'yan bindiga sun kai gagarumin hari jihar Sokoto, inda suka kashe mutane da dama.
A cewar wani mazaunin yankin da aka farmaka, maharan sun ajiye babura a gaban masallaci kafin su tarwatsa masu ibada sannan suka shiga cikin garin, inda suka kashe mutane biyar.

Source: Original
Daily Trust ta rahoto ya ce bayan sun tafi, mazauna garin suka fara shirin birne waɗanda aka kashe, sai ’yan bindigar suka sake dawowa inda suka kashe wasu mutane biyu.
“Daga nan suka fara shigowa daga wurare daban-daban, suna ta harbi ba kakkautawa tare da kewaye garin,”
In ji shi.
Ya bayyana cewa mutanen da suke cikin gidaje sun gudu, yayin da wasu suka hau wani tudu da ke garin domin tsira daga maharan.
Mazaunin ya ce shi ma ya samu damar isa tudun ta hanyar tsallake gidaje, amma daga baya ya ji ’yan bindigar suna umartar mutanensu da su kashe duk wani namiji da suka gani, yayin da suka umarce su da su bar mata da yara.
Sahara Reporters ta rahoto ya ce daga bisani maharan sun fara harbin mutanen da suka fake a kan tudun.
“Na ga wasu daga cikin mutanen da suke tare da ni a kan tudun an kashe su. Da ikon Allah, na samu damar saukowa ta bayan tudun na tsere zuwa wata gona, inda na ɓoye,”
In ji shi

Source: Facebook
An birne gawa 32 a Sokoto
Mazaunin garin ya ce ’yan bindigar sun ci gaba da kasancewa a garin har zuwa misalin ƙarfe 1:00 na dare ranar Asabar kafin su tafi, sai dai suka sake dawowa da safe suka ci gaba da kashe wasu mazauna tare da yanka wasu.
Ya ce daga baya jami’an tsaro sun isa yankin, lamarin da ya tilasta wa maharan barin garin.
A cewarsa, mazauna garin sun koma Ungushi ranar Lahadi domin neman gawarwakin waɗanda aka kashe.
“Yau wasu mutane suna gudanar da sallar jana’izar waɗanda aka kashe, yayin da wasu ke zagayawa suna neman wasu gawarwaki. Daga ƙarshe mun gano tare da birne gawarwaki 32,”
In ji shi.
An kama ɗan majalisar Osun
A wani labarin, mun ruwaito cewa jami’an rundunar ’yan sandan Najeriya sun kama ɗan majalisar dokokin Jihar Osun mai wakiltar mazabar Irewole/Isokan, Abiola Ibrahim, a Ikire bisa zargin ɓoye wasu mutane kusan 146 a gidansa.
Kama ɗan majalisar ya biyo bayan wani bidiyo da ya yadu, inda aka ga ’yan sanda suna tunkarar ɗan majalisar da wasu mutane da dama da suka taru a gidansa, waɗanda Ibrahim ya ce masu zaɓe ne.
Kakakin ’Yan Sandan Jihar Osun, DSP Abiodun Ojelabi, ya tabbatar da kama ɗan majalisar, inda ya ce an kama shi ne a Ikire bisa zargin ɓoye wasu mutane da ake zargin ’yan haya ne, tare da mutane kusan 146.
Asali: Legit.ng


