Mun fatattaki Miyagun da ke cikin Kauyukan Galbi, Damba da Kabarasha – Sojoji

Mun fatattaki Miyagun da ke cikin Kauyukan Galbi, Damba da Kabarasha – Sojoji

Rundunar sojojin Najeriya ta ce ta takawa miyagu burki a wani harin hadin-gwiwa da ta ka kai a wasu kauyukan da ke cikin karamar hukumar Chikun a yankin jihar Kaduna.

Kauyukan da dakarun su ka kai hari sun hada da Mashigi, Galbi, Damba da Kabarasha. Wannan duk ya na cikin yunkurin sojojin na ganin bayan miyagun da ke addabar jama’a.

A ranar 7 ga watan Mayu, 2020, dakarun sojojin kasar nan na Operation THUNDER STRIKE da WHIRL PUNCH su ka kai wani hari na gammaya tare da taimakon sojin sama.

Dakarun sojojin saman Operation GAMA AIKI sun taimakawa babbar rundunar wajen bankado ‘yan ta’adda da su ke labe a kauyukan na Mashigi Galbi, Damba da Kabarasha.

Kamar yadda hedikwatar sojojin kasar ta bayyana, wadannan kauyuka su na cikin yankin Gwagwada ne da ke garin Chikun. A wannan harin an hallaka miyagu akalla 17.

KU KARANTA: Sojoji sun ga bayan wani 'dan bindiga da aka dade ana nema

Bayan haka kuma jami’an sojoji sun yi nasarar harbe da-dama daga cikin masu hana Bayin Allah sakat a yankin. Wadanda aka harba sun tsere ne da raunin bindigogi a jikinsu.

Sai dai an ruguza wasu kwangon gidaje uku da wani coci a sakamakon wannan hari da aka kai. Sojojin sun bayyana cewa an yi dace babu wanda aka kashe wajen bata-kashin.

Tuni an nada wani kwamiti da zai binciki wannan tsautsayi da ya kai aka taba wurin ibada da ginin jama’a. Wannan kwamiti zai yi aiki tare da jami’an gwamnatin jihar Kaduna.

Kamar yadda dakarun su ka sanar a wani jawabi da su ka fitar a shafin Tuwita, za a biya diyya ga wadanda aka yi wa barna. Yanzu dai an samu zaman lafiya a wadannan shiyyoyi.

A jawabin rundunar, an yabawa gudumuwa da hadin kai da jama’an gari su ke badawa. Sojojin sun yi kira ga mutane su cigaba da taimakawa jami’an tsaron kasar da bayanai.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel