Bayan Gano Abin da Aka Shirya Masa, Shugaban Majalisar Dokokin Edo Ya Yi Murabus

Bayan Gano Abin da Aka Shirya Masa, Shugaban Majalisar Dokokin Edo Ya Yi Murabus

  • Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Edo, Rt. Hon Blessing Agbebaku, ya yi murabus daga mukaminsa a yau Litinin, 17 ga watan Agusta, 2026
  • Rahotanni daga jihar ta Edo sun nuna cewa Hon. Agbebaku ya sauka daga kujerar ne bayan wasu ‘yan majalisa sun shirya tsige shi
  • Mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Ivy Ebojele, ta tabbatar da murabus ɗin amma babu wani cikakken bayani kawo yanzu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Edo, Nigeria - Rahotannin da muke samu da safiyar yau Litinin, 17 ga watan Agusta, 2026 sun nuna cewa Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Edo, Rt. Hon. Blessing Agbebaku, ya yi murabus daga mukaminsa.

Bayanai sun nuna cewa Hon. Agbebaku ya dauki matakin sauka daga kujerarsa ne bayan wasu ‘yan majalisar sun shirya tsige shi.

Blessing Agbebaku.
Kakakin majalisar dokokin jihar Edo, Rt. Hon. Blessing Agbebaku a bakin aiki Hoto: Blessing Agbebaku
Source: Facebook

Kakakin Majalisar Edo ya yi murabus

Kara karanta wannan

Miji ya sakawa matarsa fetur, ya banka mata wuta ta kone

Mai taimaka wa Agbebaku kan harkokin yaɗa labarai, Ivy Ebojele, ce ta tabbatar da murabus ɗin, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito

Ebojele ta ce za a bayyana ƙarin bayanai kan dalilin da kuma yadda murabus ɗin ya kasance daga baya.

Agbebaku, wanda ke wakiltar mazaɓar Owan West, an zaɓe shi a matsayin Kakakin Majalisar Dokokin Edo ta Takwas a watan Yunin 2023.

Jagorancinsa ya fuskanci matsin lamba sosai a watan Mayun 2024 bayan ya dakatar da ‘yan majalisa uku bisa zargin cewa suna shirin tsige shi da sauran manyan jami’an majalisar.

An zaɓi sabon kakakin majalisar Edo

Hon. Yekini Idiaye, ɗan majalisar da ke wakiltar Akoko-Edo 1, ya zama sabon Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Edo.

An zaɓi Idiaye ne bisa tsarin da ya tanadi cewa idan gwamna ya fito daga Mazabar Sanatan Edo ta Tsakiya, to dole ne kakakin majalisar ya fito daga Mazabar Sanatan Edo ta Arewa.

Da yake magana da manema labarai bayan zaman majalisar na yau Litinin, sabon kakakin ya zargi magabacinsa da cin hanci da rashawa da kuma rashin gudanar da aikinsa yadda ya kamata.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Gwamnan Kebbi Ya ajiye mataimakinsa, ya dauko sabon abokin takara

Gwamnan Edo.
Gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo yana jawabi a wurin taro Hoto: Monday Okpebholo
Source: Twitter

Dalilin sauya shugabancin majalisa

A rahoton Daily Trust, Hon. Idiaye ya ce:

“An ƙaddamar da majalisar ne a ranar 16 ga Yunin 2023 ƙarƙashin jagorancin Agbebaku, kuma tun daga wannan lokaci muke fuskantar ƙalubale da dama, cin hanci da rashawa a nan da can, dage zaman majalisa, wani lokaci har na tsawon kwanaki 30 ba tare da wani dalili ba.
“Ba mu ji daɗin salon jagorancinsa ba. Jagorancinsa ya yi rauni kuma hakan yana mayar da ayyukan gwamnati baya.
“Shi ya sa muka cire shi. Dole ne mu ƙarfafa gwamnanmu mai aiki tuƙuru. Yana yin abin kirki; duk wani abu da zai kawo cikas ko dakatar da ayyukan gwamnanmu, dole ne mu dakile shi.

Gwamnan Edo ya doki yan adawar Tinubu

A wani labarin, kun ji cewa gwamnan Edo, Monday Okpebholo, ya zargi jam’iyyun adawa da amfani da matsalar rashin tsaro domin bata sunan gwamnatin shugaba Bola Tinubu.

Gwamnan Edo ya ce shugaban kasa Bola Tinubu ya yi wa Najeriya aiki fiye da wadanda suka gabace shi a shekarun da suka wuce.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262