Masu garkuwa da mutane sun fito da Kwamishinan Jihar Ekiti - Gwamnati

Masu garkuwa da mutane sun fito da Kwamishinan Jihar Ekiti - Gwamnati

- Jami’an tsaro sun ceto wani Kwamishina da aka yi garkuwa da shi a Ekiti

- Olabode Folorunso ya shafe kwanaki a hannun masu garkuwa da mutane

Kwamishinan jihar Ekiti da aka yi garkuwa da shi, Olabode Folorunso, ya samu ‘yanci daga hannun miyagun da su ka sace shi. Jaridar Punch ta ce an fito da wannan Bawan Allah.

Bayan shafe mako guda a hannun barayin mutanen, an saki Kwamishana Olabode Folorunsho ne ranar Litinin, 4 ga watan mayu, 2020, gwamnatin Ekiti ta bayyana haka.

Kwamishinan yada labarai da wayar da kan jama’a na jihar Ekiti, Muyiwa Olumilua ya bada wannan sanarwa. A jawabinsa, bai yi bayanin ko an biya miyagun kudin fansa ba.

An sace Cif Olabode Folorunso ne a ranar Lahadi, 26 ga watan Afrilu, a kan hanyar Isan zuwa garin Iludun a jihar Ekiti.

KU KARANTA: An daure wadanda su ka saci taliya da sandar sigari a Jihar Ekiti

“An fito da shi sa’o’i kadan da su ka wuce, ba tare an ji masa wani ciwo ba, kuma tuni ya koma wajen iyalinsa. Gwamnati ta godewa kaunar da jama’a su ka nuna lokacin da ya ke tsare.”

“Haka zalilka gwamnati ta yaba da kokarin da jami’an tsaro su ka yi wajen ganin an fito da shi, tare da kokarin kare rayuka da dukiyoyin jama’a da ke kan hanyoyinmu.” Inji Olumilua.

Gwamnatin Kayode Fayemi ta kuma mika ta’aziyya kan wani rashi da aka yi: “Gwamnati ta na mika ta’aziyyarta ga iyalin marigayi Olatunji Omotosho da ‘yan bindiga su ka kashe.”

Marigayi Mr Olatunji Omotosho tsohon kansila ne a jihar Ekiti wanda ya rasa rayuwarsa a ranar da aka sace wannan kwamishina. An harbe Omotosho ne yayin da ake kokarin sace shi.

Olabode Folorunso shi ne kwamishinan harkar gona a gwamnatin Dr. Kayode Fayemi. Masu garkuwa da mutane sun bukaci kudin fansa Naira miliyan 30 a lokacin da su ka sace shi.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel