Rikici ya barke tsakanin ‘Yan Sanda da Sojoji a Delta yayin da ake zaman kulle

Rikici ya barke tsakanin ‘Yan Sanda da Sojoji a Delta yayin da ake zaman kulle

Rigima ta kaure a garin Bomadi da ke cikin karamar hukumar ta Bomadi a ranar Alhamis inda har ta kai an yi jina-jina tsakanin jami’an tsaro a yunkurin dabbaka takunkumin kulle.

Jaridar The Sun ta kawo rahoto cewa an samu sabani ne tsakanin sojoji da wasu ‘yan sanda wadanda ke kokarin tabbatar da dokar kulle. Wannan sabani ya jawo har aka kai ga bude wata.

Rahotanni sun ce ‘yan sanda sun harbe wani soja wanda ya fadi a mace nan-take. ‘Yan sandan sun buda wuta ne a matsayin martani bayan wani soja ya harbi abokin aikinsu da bindiga.

Sajan Chukwudi Osuali shi ne jami’in ‘dan sandan da aka harba kuma yanzu haka ya na dakin wadanda su ke cikin halin gargara a babban asibitin gwamnati da ke garin Ughelli, jihar Delta.

Daily Sun ta ce an fara wannan rikici ne a tsakar daren Alhamis yayin da dakarun ‘yan sanda na Eagle Net Operation su ka lura cewa akwai mutanen da su ke yawo a waje sun ki shiga gida.

KU KARANTA: COVID-19: Gwamnan Enugu ya ba shugabannin kananan hukumomi umarni

Rikici ya barke tsakanin ‘Yan Sanda da Sojoji a Delta yayin da ake zaman kulle
Mai girma gwamnan jihar Delta, Sanata Ifeanyi Okowa
Asali: UGC

Wani wanda ya ke da labarin abin da ya faru ya ce ‘yan sandan sun tunkari wadannan mutane inda su ka ga cewa sojoji ne su ke shaye-shaye, a nan su ka bukaci su koma cikin barikinsu.

Wadannan sojoji sun yi wa ‘yan sandan kunnen kashi, su ka nuna cewa babu wanda ya isa ya kawo masu wargi kusa da barikinsu. Ana cikin haka ne wani soja ya harbi ‘dan sanda a ciki.

“Wannan abu na harbin abokin aikinsu ya batawa ‘yan sandan rai, wani daga cikin jami’in ‘dan sanda ya budewa sojan wuta domin ramuwar gayya, a nan take ya kashe shi.” Inji shaidan.

“Dakarun ‘yan sandan su ka yi maza su ka dauke takwaransu zuwa sashen ICU da ke babban asibitin Ughelli domin a kula da shi.” Yanzu babu labarin halin da jami’in tsaron ya ke ciki.

Shugaban dakarun sojin, Kanal Habin Manu ya yi maza ya dauki mataki. Kanal Manu ya ce hukuma za ta gudanar da bincike domin a fahimci abin da ya jawo wannan mummunar rigima.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel