Ku fara shirin ganin bayan 'Yan ta'adda – Tukur Buratai ga Dakarun Najeriya

Ku fara shirin ganin bayan 'Yan ta'adda – Tukur Buratai ga Dakarun Najeriya

Shugaban hafsun sojojin kasan Najeriya, Laftana-Janar Tukur Yusuf Buratai ya yi kira ga Dakarunsa da su yi maza su gama da yakin da ake yi da ‘Yan ta’adda a Najeriya.

Hukumar dillacin labarai ta rahoto shugaban sojojin kasan ya na wannan jawabi ne a Ranar Alhamis. Babban Sojan ya fadawa Rundunar kasar cewa ka da ta karaya a yakin.

Janar Tukur Yusuf Buratai ya bukaci Sojoji su yi amfani da damar sababbin kayan aikin da su ka samu wajen lallasa masu tada kafar baya, tare da kuma kara masu kwarin gwiwa.

Janar Buratai ya ce idan har Rundunar su ka jajirce, su ka yi na maza su ka tashi-tsaye, ‘Yan ta’addan za su zama tarihi. An dade ana yaki tsakanin Najeriya da Boko Haram.

“Kamar yadda ku ka sani, mun dauki lokaci mai tsawo a nan, kuma ina sa ran in ga mun tsaya tsayin-daka wajen ganin karshen Masu tada kayar baya a cikin kwanakin nan.”

KU KARANTA: Gwamnatin Najeriya ta sayo sababbin makamai daga kasar China

Ku fara shirin ganin bayan 'Yan ta'adda – Tukur Buratai ga Dakarun Najeriya
Janar Tukur Yusuf Buratai ya ce kwanakin 'Yan ta'adda ya zo karshe
Asali: UGC

Ya ce: “Ina mai tabbatar ma ku da cewa abin da ya rage mana kadan ne, amma akwai bukatar mu kara kokari, mu jajirce mu nuna halin maza wajen ganin bayan ragowar yakin.”

Buratai ya bayyana cewa Rundunar kasar ta karbi wasu kayan yaki da za a rabawa Dakarun da ke fadin kasar. Buratai ya na wani yawon rangadi ne domin kewaya sansanin sojoji.

A cikin zagayen da Hafsun Sojin ya ke yi, ya leka wani babban sansanin Sojojin kasa da ke Garin Molai a Yankin Chabbol da ke kusa da Maiduguri a Ranar Larabar nan da ta gabata.

Haka zalika Buratai ya gana da Sojojinsa da ke ajiye a Alau Dam har ya kuma jagoranci wata Tawaga zuwa dajin Mairimari a yankin Tamsu Ngamdua da ke Garin Mafa a Borno.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel