Matawalle ya nada madadin marigayi Sarkin Kauran Namoda
Bello Mohammed Matawallen Maradun, gwamnan jihar Zamfara, ya nada Alhaji Sanusi Mohammed a matsayin sabon sarkin masarautar Kauran Namoda.
Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da Zailani Baffa, kakakin gwamnan jihar Zamfara, ya fitar da yammacin ranar Laraba.
Ya ce gwamnan ya zabi Mohammed a matsayin sabon sarki bisa shawarar ma su ruwa da tsaki a nadin sabon sarki a masarautar Kauran Namoda.
Sabon sarkin ya maye gurbin tsohon sarki Alhaji Mohammed Ahmed Asha wanda Allah ya yi wa rasuwa ranar Lahadi, 03 ga watan Mayu, 2020.
Kafin nadinsa a matsayin sabon sarki, Mohammed, mai shekaru 40 a duniya, manjo ne a rundunar sojin Najeriya.
Mohammed da ne wurin marigayi Asha, kuma shi ne sarkin yanka na biyu a tsarin sarki mai sanda a masarautar, amma ku ma sarki na 16 a tsarin masarautar Kiyawan Kauran Namoda.

Asali: UGC
Da safiyar ranar Lahadi ne Legit.ng ta wallafa labarin mutuwar Sarkin masarautar Kauran Namoda a jihar Zamfara, Alhaji Muhammad Ahmad Asha.
Sarkin ya rasu ne da safiyar ranar Lahadi, 3 ga watan Mayun 2020 bayan fama da gajeriyar rashin lafiya kamar yadda wani na kusa da fadar sarkin ya tabbatar wa BBC.
DUBA WANNAN: Ganduje ya nada Kabiru Inuwa a matsayin sabon sarkin masarautar Rano
Ya rasu yana da shekaru 71 a duniya, ya kuma bar mata uku da yaya da dama.
A cewar jaridar The Punch, Sarkin ya mutu ne a asibitin da aka killace shi.
Jaridar ta ce ya ana zargin cewa cutar covid-19 ce ta yi sanadin mutuwarsa.
The Punch ta ce sakataren yada labarai na kwamitin yaki da cutar covid-19 a jihar Zamfara, Mustafa Jafaru, ya ce basaraken ya na killace ne a asibitin kwararru da ke garin Gusau, babban birnin jiha.
Jafaru ya bayyana cewa an dauki jininsa tare da aika shi zuwa dakin gwaji a Abuja, amma har ya zuwa yanzu sakamakon gwajin bai fito ba.
Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Sani Yariman Bakura, ne ya nada marigayin a matsayin sarki mai sanda na masarautar Kauran Namoda a shekarar 2004.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng