Katsina: ‘Yan bindiga sun hallaka mutane 47 a Danmusa da Dutsinma – Inji ‘Yan Sanda
A daidai lokacin da ake fama da annobar cutar COVID-19, rundunar ‘yan sandan jihar Katsina sun tabbatar da kisan mutane rututu da aka yi kwanan nan a wasu kauyukan jihar.
Kakakin ‘yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isa ya ce: “A ranar 18 ga watan Afrilun 2020 da kimanin karfe 1:20 na tsakar dare, wata bataliyar ‘yan bindiga dauke da makaman AK-47 su ka kai hari a kauyen Kurechi da ke cikin karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina.”
SP Isa a madadin dakarun ‘yan sandan ya kara da cewa: “Mutanen kauyen sun yi namijin kokari sun fatattaki wadannan ‘yan bindiga. Daga bayan kauyawan su ka rika kona totuwan masara domin su kare dabbobinsu da kuma kawunansa daga ta’adin wadannan miyagu.”
Duk da kokarin da wadannan Bayin Allah su ka yi, labarin ya canza a lokacin da ‘yan bundigan su ka shiga kona wurare a kauyen Aibon Mangwaro da ke karamar hukumar Danmusa.
KU KARANTA: Ana zargin COVID-19 ta shigar Borno bayan Malamin lafiya ya mutu
“A kauyen Kurechin Atai da ke cikin garin Danmusa, an kashe mutane 14. An kuma kashe mutane 4 da 6 tsakanin kauyukan Kurechin Giye da kuma Kurechin Dutse da ke Dutsinma.”
Wannan barna ba ta tsaya nan ba, a kauyukan Makauwachi da Daule, ‘yan bindiga sun kashe mutane 19 da kuma 4. Kakakin ‘yan sanda ya shaida wannan a cikin karshen makon nan.
Isah ya tabbatar da cewa kawo yanzu an tada dakaru na musamman zuwa wannan yanki domin ganin bayan miyagun da su ka addabi mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba.
Dakarun da aka aika zuwa yankunan na Katsina sun kunshi jami’an sojojin sama da sojojin kasa, da kuma jami’ar NSCDC. Haka tawagar ta na kunshe da jami’an tsaro masu fararen kaya.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng