Miji Ya Sakawa Matarsa Fetur, Ya Banka Mata Wuta Ta Kone
- Rundunar ‘yan sandan jihar Kogi ta kama wani malamin makaranta, Jacob Irewa, bisa zargin zuba wa matarsa, Berida Irawo, fetur tare da cinna mata wuta
- An ce lamarin ya faru ne ranar Juma’a da rana a gidansu da ke Oworo, Felele, Lokoja, sakamakon rashin jituwa da ta taso kan wasu rigunan mijin
- Mijin ya ce matarsa ta ƙona rigunan ne bayan ya matsa mata ta bayyana inda suka shiga, lamarin da ya sa ya fusata har ya kunna mata wuta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kogi – Rundunar ‘yan sandan jihar Kogi ta kama wani malamin makaranta, Jacob Irewa, bisa zargin yunƙurin kashe matarsa, Berida Irawo, ta hanyar zuba mata fetur da cinna mata wuta.
Lamarin ya faru ne a ranar Juma’a, 14 ga watan Agusta 2026, a gidansu da ke unguwar Oworo, Felele, Lokoja, bayan wata takaddama ta cikin gida.

Source: Original
Daily Trust ta ruwaito cewa rikicin ya samo asali ne bayan Irewa ya gano cewa wasu daga cikin rigunansa masu gajeren hannu sun ɓace, lamarin da ya haifar da rashin jituwa tsakaninsa da matarsa.
Miji ya kona matar shi
Irewa ya ce ya dawo daga waje, ya yi wanka, sannan ya nemi sanya ɗaya daga cikin rigunansa masu gajeren hannu guda bakwai da ya fi so, amma bai same su a cikin ɗakinsa ba.
Ya ce bayan ya bincika wurare daban-daban, ciki har da wurin da suke shanya kaya a bayan gidan, sai ya tambayi matarsa game da rigunan.
A cewarsa, matarsa ta fita daga ɗakin tana mai cewa ta ƙona rigunan bayan ya matsa mata da ta bayyana abin da ta yi.
Ya ce daga nan ne ya fusata, ya je inda ya ajiye babur dinsa, ya ɗauko fetur ya zuba wa matarsa sannan ya kunna mata wuta da ashana.
“Ban san yadda abin ya faru ba; Allah Ya yi mini rahama,”
In ji shi.
Irewa ya kuma bayyana kansa a matsayin fasto, sannan malamin makaranta ne a ƙauyen Irawo, inda yake hutun aiki a Lokoja.
Ya yi ikirarin cewa bai taɓa faɗa da matarsa kan wani abu ba, tare da cewa sun shafe shekaru da aure ba tare da samun ɗa ba.
‘Yan sanda sun fara bincike
Punch ta wallafa cewa rundunar ‘yan sandan Kogi ta ce ta samu rahoton lamarin da misalin ƙarfe 8:30 na dare ranar Juma’a.
Mai magana da yawun rundunar, ASP Saliu Oyiza Afusat, ta ce binciken farko ya nuna cewa rikicin ya samo asali ne bayan matar ta ƙona wasu daga cikin tufafin mijinta da ta yi imanin ba ya amfani da su, ba tare da izininsa ba.

Source: Twitter
Afusat ta ce wanda ake zargin ya amince a bayanansa cewa shi ne ya cinna wa matarsa wuta, yayin da rundunar ta fara cikakken bincike domin gano cikakkun bayanan lamarin da kuma tattara ƙarin hujjoji.

Kara karanta wannan
Tsautsayi ya faɗa kan matar aure da 'ya'yanta 2 cikin dare, Allah ya musu rasuwa a Kaduna
An zubata mai ciki ruwan zafi
A wani labarin, mun ruwaito cewa rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta kama wata mata mai shekara 20, Rabi Abubakar, bisa zargin zuba wa kishiyarta mai juna biyu tafasasshen ruwa.
An ce lamarin ya faru ne ranar 17 ga watan Yulin 2026, inda aka garzaya da matar da abin ya shafa zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi domin samun magani.
‘Yan sandan sun ce duk da munanan raunukan da ta samu, matar ta haifi ɗa namiji yayin da take karɓar magani a ranar 19 ga Yuli, sai dai jaririn ya rasu daga bisani.
Asali: Legit.ng

