Shugaban Sojojin Najeriya
Da alamu jawabin Mai garkuwa da mutanen nan Hassan Wadume ya jefa Sojoji cikin matsala. Watakila a kori wasu Sojojin Najeriya daga aiki a kan wannan mai laifi da a ke kira Wadume.
Shugaban Rundunar Operation Lafiya Dole ta Sojojin Najeriya, da ke yaki da 'yan ta'adda a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya, Olusegun Adeniyi, ya ce rundunarsa za ta mayar da hankali kan dakile hanyoyin kudin Boko Haram.
Mun ji labari cewa Jami’in Soja ya bar wani kasurgumin mai laifi ya tsere a Taraba. Sojojin sun maida mai laifin da ‘Yan Sanda su ka kama. Wani Kyaftin din Soja ne ya yi wannan aiki a Garin Ibbi.
Rundunar Sojan kasa ta gudanar da jana’izar dakarunta guda 5 a ranar Juma’a, wadanda suka mutu a yayin arangama da mayakan kungiyar ta’addanci na Boko Haram a yankin Arewa maso gabashin Najeriya.
A na zargin Dakarun Sojoji sun sha giya sun harbe mutane har lahira. Bayan kisan ‘Yan Sanda, Sojoji sun kuma hallaka wasu mutane a Legas inda ya jawo a ka sake samun sabani tsakanin ‘Yan Sanda da Sojoji.
Binciken da rundunar Yansandan Najeriya ta kaddamar ya bankado dadaddiyar alaka tsakanin wani hafsan Soja mai mukamin kyaftin da kasurgumin barawon mutanen nan da ake nema wurjanjan a jahar Taraba, Hamisu Bala Wadume.
Rundunar Sojan Najeriya ta aika da wasu sababbin motocin yaki guda hudu na musamman zuwa bakin daga a yankin Arewa maso gabashin Najeriya don kara ma yaki da yan ta’addan Boko Haram kaimi.
Sojojin saman Najeriya sun yi abin a yaba inda Sojoji su ka yi luguden wuta a wuraren da Boko Haram su ka labe. Rundunar Sojin sama sun kai wannan hari ne a Ranar ja-ji-birin Sallah.
A yayin tumke damarar tabbatar da ingancin tsaro domin bunkasa harkokin yaki da ta'addanci a Najeriya, manyan dakarun sojojin 13 na kasar Amurka na ci gaba da zagaye da kuma gudanar da ziyarce-ziyarce a Najeriya.
Shugaban Sojojin Najeriya
Samu kari