Shugaban APC zai Hada Mutum Miliyan 1 Su Zabi Tinubu a Ondo a 2027
- Shugaban APC na jihar Ondo, Babatunde Kolawole, ya ce jam’iyyar ba ta rabu ba duk da wasu saɓanin ra’ayi da ake samu tsakanin mambobinta
- Kolawole ya bayyana cewa an kafa kwamitin sulhu domin sasanta ɓangarorin da ke da saɓani tare da tabbatar da haɗin kan jam’iyyar kafin zaɓuka masu zuwa
- Shugaban APC ɗin ya ce jam’iyyar na da burin samun aƙalla kuri’u miliyan ɗaya ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu a jihar Ondo a zaɓen shugaban ƙasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Akure – Shugaban jam’iyyar APC a jihar Ondo, Babatunde Kolawole, ya ce babu rabuwar kai a cikin jam’iyyar duk da wasu saɓanin ra’ayi da suka taso tsakanin mambobinta.
Kolawole, wanda tsohon ɗan majalisar wakilai ne, ya bayyana cewa irin waɗannan saɓani al’amura ne da suka saba faruwa a siyasa, yana mai cewa jam’iyyar na da hanyoyin cikin gida da take amfani da su wajen warware matsalolin.

Source: Facebook
A wata hira da jaridar Punch, Kolawole ya ce shugabancin jam’iyyar ya fara ƙoƙarin ƙarfafa tsarin APC a jihar bayan zaɓensa a matsayin shugaban jam’iyyar, duk da yawan ayyukan siyasa da suka biyo baya.
APC ta musanta rabuwar kai
A hirar da aka yi da shi, Kolawole ya ƙi amincewa da raɗe-raɗin cewa APC na neman rabuwa gida biyu a jihar Ondo.
Ya ce:
“Ban yarda cewa jam’iyyar ta rabu a jihar ba. A wurina, waɗannan ƙananan matsaloli al’amura ne na siyasa. Saɓanin ra’ayi ne na siyasa, kuma ba su da ƙarfi har su raba mu a matsayin jam’iyya.”
Ya bayyana cewa bayan kammala zaɓukan fiyar da gwani na jam’iyyar, shugabancin APC ya ɗauki matakan da suka dace domin duba sakamakon zaɓukan.
A cewarsa, an kafa wani kwamiti da ya yi nazari kan yadda zaɓukan fitar da gwani suka gudana, sannan kwamitin ya miƙa rahotonsa ga shugabancin jam’iyyar na ƙasa, wanda daga bisani ya ɗauki wasu matakai.

Kara karanta wannan
'Yan takarar shugaban ƙasa 3 sun haɗa kai domin ƙwace mulki daga hannun Tinubu a 2027
APC na neman kuri’u miliyan 1
Kolawole ya bayyana cewa babban abin da jam’iyyar ta fi mayar da hankali a kai shi ne ganin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya samu nasara a zaɓen shugaban ƙasa.
Ya ce Gwamnan jihar Ondo ya riga ya bayyana a hukumance cewa jihar na tare da Tinubu, yayin da jam’iyyar kuma ta sa samun aƙalla kuri’u miliyan 1 ga shugaban ƙasar.
“Gwamna ya sanar cewa jihar Ondo ta Tinubu ce. Muna da burin samar da aƙalla kuri’u miliyan ɗaya ga Shugaban Ƙasa, kuma za mu haɗa ƙarfi da karfe domin tabbatar da hakan,”
In ji shi.

Source: Facebook
APC: Batun yada labaran karya
A wani labarin, mun ruwaito cewa wani jigo a APC, Dr Femi Alabi, ya yi gargadin cewa yaɗuwar bayanan ƙarya na iya yin barazana ga tafiyar Tinubu
Alabi ya bayyana hakan ne a Abuja yayin ƙaddamar da masu kula da yada manufar Tinubu/Shettima yayin taron masu fada a ji na jam'iyyar APC.
Ya ce matsin tattalin arziki da kuma rashin ingantaccen tsarin sadarwa na iya hana ganin nasarorin gwamnatin, yana mai jaddada cewa shugabanci nagari na buƙatar riƙon amana.
Asali: Legit.ng
