Harkar tsaro: Ya kamata a gayyato Shugaba Buhari zuwa Majalisa – Inji PDP

Harkar tsaro: Ya kamata a gayyato Shugaba Buhari zuwa Majalisa – Inji PDP

A Ranar Lahadi ne jam’iyyar hamayya ta PDP ta yi kira ga Majalisar tarayya da ta gayyaci shugaban kasa Muhammadu Buhari zaurenta da zarar ta dawo hutu.

PDP ta na so shugaban kasa Muhammadu Buhari ya zo ya yi wa ‘Yan majalisa bayanin irin kokarin da yake yi na shawo kan sha’anin tsaro da ya ke ta faman tabarbarewa.

A akon nan ne ‘Yan majalisa za su dawo dogon hutun karshen shekara da su ka tafi, don haka PDP ta ke ganin zai yi kyau a fara aiki da gayyatar shugaban kasa a majalisar.

Jam’iyyar adawar ta yi wannan jawabi ne ta bakin babban Sakataren yada labaranta na kasa, Kola Ologbondiyan, wanda ya koka da halin rashin tsaron da aka shiga a yau.

“Matsayar Jam’iyyar mu ita ce sha’anin tsaro ya fi karfin a sa siyasa da bangaranci da kuma furofaganda a ciki, abu ne wanda ake bukatar masu ruwa da tsaki su zauna.”

KU KARANTA: Buhari ya bada umarni ayi wa 'Yan bindiga luguden wuta

Harkar tsaro: Ya kamata a gayyato Shugaba Buhari zuwa Majalisa – Inji PDP
PDP ta ce harkar tsaro ya fi karfin gwamnatin Shugaba Buhari
Asali: Facebook

PDP ta na ganin lokaci ya yi da yanzu za “A duba tsarin tsaron Najeriya da kuma hanyar da Mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari yake bi na shawo kan matsalar.”

A cewar PDP, alkaluman da cibiyar tattalin arziki da zaman lafiya ta Duniya su ka fitar na cewa Najeriya ce ta uku a wajen ta’addanci a fadin Duniya ya na da ban tsoro.

Rahoton da cibiyar ta fitar a shekarar 2019 ya nuna cewa kasashen Afganistan da Iraki ne kurum su ka sha gaban Najeriya wajen hare-haren ta’addanci a kasashen Duniya.

Kola Ologbondiyan a jawabin da ya fitar a Ranar 26 ga Watan Junairun 2020 ya ke cewa rahoton IEP ya tabbatar da abin da PDP ta dade ta na fada a kan harkar tsaron kasar.

Mista Ologbondiyan ya ke cewa matsayar su ita ce tsare rayuka da dukiyoyin mutanen Najeriya ya zama abin da ya fi karfin gwamnatin Buhari duk da tarin alkawarin da ta yi.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng