Tsaro: Abinda Buhari ya fada wa shugabannin rundunonin tsaro na kasa yayin ganawarsu

Tsaro: Abinda Buhari ya fada wa shugabannin rundunonin tsaro na kasa yayin ganawarsu

A ranar Alhamis ne fadar shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ta yi watsi da jita - jitar da wasu 'yan Najeriya ke yada wa a kan cewa taron gaggawar da shugaba Buhari ya kira shugabannin rundunonin tsaron nada alaka da kiran da wani sanata ya yi a kan Buhari ya yi murabus saboda gazawarsa a bangaren tsaro.

A ranar Laraba ne Sanata Eyinnaya Abaribe, mamba a majalisar dattijai, ya yi kira ga shugaba Buhari da ya yi murabus saboda ya gaza shawo kan matsalolin tsaro da suka addabi sassan Najeriya.

Sai kuma gashi a ranar Alhamis shugaba Buhari ya kira wani taro na gagga wa da shugabannin rundunonin tsaro na kasa a fadarsa, lamarin da yasa wasu suke zargin cewa taron ba zai rasa nasaba da kiran neman Buhari ya yi murabus ba.

A wata hira da ya yi da sashen Hausa na BBC, kakakin shugaban kasa, Malam Garba Shehu, ya ce ko kadan babu gaskiya a zargin da wasu da keyi a kan cewa taron yana da alaka da kalaman Abaribe.

Tsaro: Abinda Buhari ya fada wa shugabannin rundunonin tsaro na kasa yayin ganawarsu
Buhari da shugabannin rundunonin tsaro na kasa yayin ganawarsu ranar Alhamis
Asali: Twitter

"An shirya taron ne tun kafin kalaman shi Sanatan da ake magana a kansa, taro ne da aka saba shirya wa daga lokaci zuwa lokaci ko kuma duk lokacin da bukatar hakan ta taso kamar yadda aka saba," a cewar Garba Shehu.

DUBA WANNAN: Ka cancanci a daureka a kurkuku - Buhari ya mayar da martani ga Sanata Abaribe

Kazalika, ya karyara zargin cewa shugaba Buhari ya gaza shawo kan matsalolin tsaro a sassan Najeriya.

"Ba iya Najeriya ce ke fuskantar kalubalen tsaro ba, matsala ce da ta addabi kasashen da ke yankin Sahel, kuma dukkan kasashen yankin sun hada kai, suna aiki tare domin ganin sun samu nasara yakar laifukan ta'addanci da 'yan ta'adda," a cewar Garba Shehu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel