Shugaban NSCDC ya bukaci ayi bincike a kan kisan Ndubuisi Emenike

Shugaban NSCDC ya bukaci ayi bincike a kan kisan Ndubuisi Emenike

Shugaban Rundunar Jami’an tsaro ta NSCDC, Abdulahi Gana Muhammadu ya bukaci a gudanar da cikakken bincike a game da kisan Ndubuisi Emenike.

Kwanakin baya ne wani jami’in hukumar ya harbi Mista Ndubuisi Emenike, wanda fitaccen ‘Dan siyasa ne a jihar Imo. Wannan ya yi sanadiyyar ajalinsa.

NSCDC ta bayyana cewa za a bi diddikin abin da ya yi sanadin mutuwar wannan fitaccen ‘Dan siyasa. Hukumar ta fitar da wannan jawabi ne a jiyan nan.

Emmanuel Okeh wanda ya ke magana a madadin NSCDC, a jawabin da ya fitar Ranar Litinin, ya ce shugaban hukumar ya bada umarni a soma bincike.

Abdulahi Gana Muhammadu ya bayyana mutuwar wannan Bawan Allah a matsayin rashi mai ban takaici ga Iyalinsa Mamacin da kuma mutanen jiharsa.

KU KARANTA: An sake nada Gwamna Bello a kan gadon mulkin jihar Kogi

Shugaban NSCDC ya bukaci ayi bincike a kan kisan Ndubuisi Emenike
Jami'in NSCDC ya hallaka wani 'Dan siyasa a Jihar Imo
Asali: Facebook

A cewar Gana Muhammadu, Najeriya gaba daya za ta yi rashin Marigayin, ya na mai nuna takaicinsa ga wannan mummunan abu da ya riga ya auku.

“Kawo yanzu an kama Jami’in da ya yi wannan danyen aiki, an mika sa gaban ‘Yan Sanda. Za a bi ka’ida wajen ganin an hukunta shi yadda doka ta ce.”

Jawabin ya ce: “Shugaban ya kara da bada umarni ga Shugaban shiyya ta E na Yankin Owerri da kuma Shugaban jihar Imo, su gudanar da cikakken bincike.”

“Bayan haka su tabbata doka ta yi aiki da kyau wajen hukunta wannan jami’i domin ya zama darasi ga sauran Jami’an hukumar.” Inji Gana Muhammadu.

NSCDC ta gargadi shugabannin Jihohi su dage wajen ganin ba a sake samun faruwar irin wannan hadari ba, tare da tabbatar da cewa za a rika korar mugun iri.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel