Mu na nan a kan bakarmu na tsige Hafsun Sojoji – Majalisar Wakilai
Majalisar wakilan tarayya ta ce har yanzu ta na kan matsayar ta na cewa dole shugabannin hafsun sojojin Najeriya su yi murabus, ko kuma a tsige su.
Mai magana da yawun bakin ‘Yan majalisar wakilan kasar shi ne ya kara jaddada wannan matsaya da su ke kai a cikin karshen makon nan da ya wuce.
Honarabul Benjamin Kalu ya ke cewa Majalisar ba ta lashe amanta game da matakin da ta dauka na cewa a nada wasu sababbin hafsun sojoji a Najeriya ba.
Kalu ya fadawa ‘Yan jarida: “Ku na cikin Majalisar, kun ji wani ya tashi ya bukaci a janye wannan matsaya? Matsayarmu ta na nan, ba mu lashe amanmu ba.”
Hon. Kalu ya kara da: “Kun san aikin majalisa, kun san abin da mu ke yi, Idan har an cin ma wata matsaya, kuma ana so a canza ta, akwai hanyar da ake bi.”
KU KARANTA: 'Yan sun cafke ‘Yan Ansaru da ke da hannu wajen garkuwa da mutane
“Majalisa ta dauki wannan mataki. Don haka duk matsayar da mu ka cinma, ta na nan har sai ranar da wani ya bukaci a janye wannan mataki” Inji Kalu.
Kwanakin baya, Majalisar ta tsaida magana cewa a canza shugabannin sojoji domin a kawo karshen kashe-kashen da ake fama da shi a halin yanzu.
Benjamin Kalu, wanda ya ke magana a madadin ‘Yan majalisa ya ce ka da wanda ya yi tunanin sun sauko daga matsayar da su ke kai game da harkar tsaro.
Tun a shekarar 2015, shugaba Buhari ya nada hafsun soji wanda har yau bai canza su ba duk da cewa a doka, dukkaninsu sun zarce shekarun da ake yi a aiki.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi
https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng