An yi garkuwa da wasu mutane har da wani Limamin Sarkin Borgu

An yi garkuwa da wasu mutane har da wani Limamin Sarkin Borgu

Kwanaki kadan bayan umarnin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada na yi wa Yankunan jihar Neja luguden wuta, an sake kai wasu hare-haren.

A wani danyen hari da ‘Yan bindiga su ka kai a kwanan nan, sun hallaka mutum daya, sun kuma tsere da mutane akalla 20, bayan wasu uku da aka yi wa rauni.

Jaridar Daily Trust ta bayyana cewa an kai wannan hari ne a karamar hukumar Borgu, wanda a sanadiyyar haka aka sace wani Malami mai suna Malam Habibu.

Malam Habibu ya na cikin Limamin fadar Sarkin Borgu. Garkuwa da Bayin Allah ya sa mai martaba Sarki Muhammad Halliru Dantoro ya kira taron gaggawa.

An bukaci Sarkin Borgu ya biya Miliyan 20 kafin a a saki Limamin. An ji labarin wadannan Miyagun sun kai irin wannan hari a gidan shakatawa da ke Wawa.

KU KARANTA: An gano bayanai game da wanda ya nemi ya dasa bam a coci

An yi garkuwa da wasu mutane har da wani Limamin Sarkin Borgu
Duk da umarnin Buhari, an sace wani babban Limamin Sarki Dantoro
Asali: Twitter

Miyagun sun kai wannan hari ne a Ranar Asabar, 1 ga Watan Fubrairun 2020, da kimanin karfe 5:30 na yamma. Kusan wannan ne harin farko da aka kai a Garin.

“Sun kai wa mutanen da ke dawowa daga kasuwanni hari bayan sun tare hanyar Ibbi zuwa New Bussa.” Wani Bawan Allah ya bada labarin yadda abin ya faru.

A cewar Majiyar, ‘Yan bindigan su na dauke ne da makamai da su ka hada da bindigogi da adda da wukake. Su na da yawa, sannan kuma sun zo ne a kan babura.

Wadanda su ka yi wannan aiki sun sake shigowa cikin Garin na New Bussa a Ranar Lahadi. Amma a wannan lokaci ba su taba kowa ba, sai dai aka yi ta addu’a.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel