Abinda yasa kawo karshen kungiyar Boko Haram ya yi wuya - Buratai

Abinda yasa kawo karshen kungiyar Boko Haram ya yi wuya - Buratai

Laftanal Janar Tukur Yusuf Buratai, babban hafsan rundunar sojojin kasa, ya ce shugabannin kungiyar Boko Haram da masu yi musu farautar sabbin mambobi suna rayuwa ne kamar kowa a cikin sauran jama'a, lamarin da yasa gano su ya ke matukar wahala.

Buratai ya bayyana cewa salon yakin sunkuru da Boko Haram ke amfani da shi da kuma amfani da farfaganda da riko da akidun rikau sun saka kungiyar yin nisan kwana.

A wata hira da ya yi da jaridar Daily Trust, Buratai ya bayyana cewa an samu cigaba a yaki da kungiyar Boko Haram idan aka kwatanta da shekarun baya, amma ya amince da cewa kungiyar ta dan farfado a 'yan kwanakin baya bayan nan.

"Ba zaka yaki ta'addanci ba sannan ya tafi gaba daya a lokaci guda, 'yan ta'adda sauya salo suke yi koda yaushe. Haka ta'addancin yake," a cewarsa.

Sannan ya cigaba da cewa, "suna yada farfaganda domin nuna cewa duk wani kokari na hukumomin tsaron gwamnati bashi da tasiri a kansu. Yin hakan yana daga cikin dabarunsu. Suna fake wa da raunin tattalin arzikin jama'a da banbancin siyasa wajen yada kiyayya da gaba a tsakanin mabanbantan addinai da kabilu.

Abinda yasa kawo karshen kungiyar Boko Haram ya yi wuya - Buratai
Buratai
Asali: Depositphotos

"Shi yasa suke tare hanya tare da kama mutanen da ba addininsu daya ba, sannan su kashe su, su kuma aika wa duniya. Wannan salo ne na farfaganda da 'yan ta'adda suke amfani da shi.

DUBA WANNAN: Saurayi ya ci 100m a cacar da ya shiga da kudin budurwarsa 10k, rigima ta barke bayan ya bata iya kudinta 10k

"Zaka iya zama tare da su ba tare da sanin cewa 'yan ta'adda bane. Suna da 'yan leken asiri da masu kai musu duk irin kayayyakin da suke bukata. Suna da wasu shugabannin da ke zaune a cikin kauyuka da garuruwa tare da sauran jama'a, kuma sune ke bayar da bayanai ga sauran shugabannin da ke boye a daji. Ta hakan ne suke samun damar shirya kai hari sannan su koma maboyarsu".

Hafsan rundunar sojin ya kara da cewa mayakan kungiyar Boko Haram sun fara daukan makami ne a shekarar 2009 amma an samu kusan shekaru 40 da cusa wa mayakan kungiyar akidar da suke kai har yanzu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel