Da sake: Tsarin tsaronmu ya gaza fitar da mu – Shugaban Majalisa, Lawan

Da sake: Tsarin tsaronmu ya gaza fitar da mu – Shugaban Majalisa, Lawan

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Ibrahim Lawan, ya ce tsarin tsaron da ke aiki da aiki da shi a Najeriya ya gagara kawo zaman lafiyan da ake bukata.

Sanata Ahmad Ibrahim Lawan ya nuna cewa akwai bukatar ayi wa tsarin da ake tafiya a kai garambuwal domin a samu kwanciyar hankali a kasar.

Ahmad Ibrahim Lawan ya yi wannan bayani ne a lokacin da ya zanta da Manema labarai a Abuja. Shugaban majalisar ya yi wannan hira ne a Ranar Litinin.

Sanatan ya ce kashe-kashen da aka dawo da shi da kuma satar mutane, ya sa dole Majalisa za ta dauki matsaya game da irin kamun ludayin jami’an tsaro.

“Za mu zauna da Jami’an tsaro a Majalisar dattawa domin mu ji abin da ya sa harkar tsaro ya ke kara tabarbarewa a bangarori da-dama da ke kasar.”

KU KARANTA: Wata Baiwar Allah ta kashe Mijinta a Jihar Katsina

Da sake: Tsarin tsaronmu ya gaza fitar da mu – Shugaban Majalisa, Lawan
Shugaban Majalisa Ahmad Lawan ya ce sai an canzawa tsarin tsaro zani
Asali: Twitter

“Mun gana a baya, amma barkewar rashin tsaro ya sa yanzu za mu fitar da matsaya a matsayin mu na ga gwamnati, ba za su yi wasa da tsaro ba.”

Lawan ya ke cewa tsaron rayuka da dukiyar jama’a ba abu ba ne da za a sa siyasa a ciki. Sanatan ya sha alwashin cewa za su yi kokarin gyara lamarin.

“Don haka Majalisa za ta dauki matsayar yadda ya kamata tsaron kasa ya kasance. Mu na ganin cewa sai an sakewa ginin da aka yi wa tsaro zani.”

“Ko ta gwamnatin tarayya ne, ko jiha ko karamar hukuma ko Sarakuna ko wasu, muhimmin abu shi ne a kare rayukan jama’a da kuma dukiyoyinsu.”

Dr. Lawan ya koka da halin da ake ciki ne musamman bayan hare-haren da aka kai a hanyar Borno zuwa Yobe da wasu sassan a ‘yan kwanakin nan.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng