Raymond Dokpesi ya fara kare kansa a shari’ar badakalar N2.1b

Raymond Dokpesi ya fara kare kansa a shari’ar badakalar N2.1b

A Ranar Talata, shugaban kamfanin sadarwa na DAAR, Raymond Dokpesi, ya fara kare kansa a gaban babban kotun tarayya da ke Garin Abuja.

A makon nan Cif Raymond Dokpesi ya fare kare kansa a zargin da hukumar EFCC ta ke yi masa na hannu wajen satar wasu kudi Naira biliyan 2.1.

EFCC ta jefi Raymond Dokpesi da zargin aikata laifuffuka bakwai da ke da alaka da karbar kudi daga hannun tsohon NSA, Kanal Sambo Dasuki.

Babban Lauyan da ke kare hukumar EFCC, Rotimi Jacobs SAN, ya fadawa kuliya cewa Raymond Dokpesi zai fara kare kansa a gaban Alkalin kotu.

Rahotanni sun ce Mike Ozekhome SAN wanda ke kare wanda ake tuhuma, ya kira shi da kansa Dokpesi ne a matsayin shaidan farko a shari’ar.

KU KARANTA: EFCC: An koma gaban Alkali da tsohon Minista Fani-Kayode

Raymond Dokpesi ya fara kare kansa a shari’ar badakalar N2.1b
EFCC ta ce Raymond Dokpesi ya karbi kudi a hannun Sambo Dasuki
Asali: UGC

A na sa jawabin, Dokpesi ya fadawa kotu cewa ainihinsa kwararren Injiniyan ruwa ne sannan shugaban babban kamfanin sadarwar nan na DAAR.

Wanda ake zargi, ya shaidawa kotu cewa ya shafe shekaru kamar 30 ya na aikin yada labarai, inda ya yi hulda da gwamnati a matakai daban-dabam.

“Abin da masu kasuwanci da mu su ke bukata kawai shi ne, su same mu ta bakin ma’aikatan hada-hadanmu da jami’ai, a yanki lokacin tallan da ake so.”

“Babu wata saniyar ware wajen aikinmu, mu na daukar kowa daya." Inji Dokpesi. A karshe Alkali John Tsoho ya dage shari’ar zuwa Yau watau Laraba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel