Kungiyar CHRSJ ta yi kaca-kaca da Gwamnatin Buhari game da sha’anin tsaro

Kungiyar CHRSJ ta yi kaca-kaca da Gwamnatin Buhari game da sha’anin tsaro

Wata cibiya mai kokarin kare hakkin Bil Adama da tabbatar da adalcin rayuwa a Najeriya, CHRSJ, ta fito ta yi magana game da sha’anin tsaro.

Kungiyar CHRSJ ta gargadi shugaban kasa Muhammadu Buhari ya daina yi wa jama’a karya game da halin da ake ciki na rashin tsaro a halin yanzu.

Shugaban CHRSJ, Adeniyi Sulaiman, a wani jawabi da ya fitar, ya bayyana cewa halin da Najeriya ta ke ciki ya sha ban-ban da abin da gwamnati ke fada.

Adeniyi Sulaiman ya fitar da jawabi a jiya Ranar Laraba ya na bayyana matsayar kungiyar tare da yi wa Mai magana da yawun shugaban kasar raddi.

Sulaiman ya na ganin cewa maganar da fadar shugaban kasa ta ke yi na cewa an samu tsaro idan aka kamanta da shekarar 2015, sam ba gaskiya ba ne.

Kungiyar ta ce idan za a tuna, shekarun baya Ministan yada labarai da al’adu, Lai Mohammed, ya fadawa ‘Yan Najeriya an ci karfin ‘Yan Boko Haram.

KU KARANTA: Shashanci ne a rika kiran in yi murabus - Inji Buhari

A lokacin Ministan ya san cewa shugaban kasar ya fadawa ‘Yan Najeriya abin da zai masu dadi ne kawai a game da yakin da ake yi da ‘Yan ta’addan.

CHRSJ ta na goyon bayan majalisar datttawa na cewa akwai gyara a tsarin gidan Soji da kuma yadda aikin ‘Yan Sanda da sauran jami’an tsaro yake.

A dalilin haka, Adeniyi Sulaiman, ya yi kira da a sakewa tsarin Jami’an tsaro zani, domin a na sa ganin, wannan tsari ba zai kai kasar ga zaman lafiya ba.

Bayan haka, CHRSJ ta bukaci shugaban kasa ya sauke gaba daya Hafsun Soji a sakamkon karfin da ‘Yan ta’adda da ‘Yan bindiga su ke kara yi a yanzu.

A karshe, Sulaiman ya jinjinawa Enyinnaya Abaribe a kan kiran da ya yi na shugaban kasa Buhari ya yi murabus, tare da kiran gwamnati ta tashi tsaye.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel