‘Yan Sanda sun kama wanda ya hallaka ‘Danuwansa saboda IPhone 11 a Anambra

‘Yan Sanda sun kama wanda ya hallaka ‘Danuwansa saboda IPhone 11 a Anambra

Jami’an ‘Yan Sanda a jihar Anambra sun kama wani Bawan Allah bisa zargin kashe ‘Danuwansa daya da ya ke da shi a Duniya saboda ya gaji wayarsa.

Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya sun bayyana sunan wannan Matashi mai shekaru 26 a Duniya da Paul, kamar yadda mu ka samu labari a Ranar Laraba.

Paul ya shaidawa Manema labarai a lokacin da aka yi hira da shi cewa shaidan ne ya sa ya kashe ‘Danuwan na sa don kurum ya samu damar gaje wayarsa.

Mista Paul ya bayyanawa ‘Yan jarida a lokacin da ake hira da shi cewa babu ce ta sa yayi wannan aiki saboda ya gaji da shan gori daga wurin Abokansa.

A cewarsa Abokansa kan yi masa izgili ganin bai da halin sayen wayar salular. Bayan takaicin ya yi masa yawa, sai ya yanke shawarar ya kashe ‘Danuwansa.

KU KARANTA: Gwamna zai hana gaba daya Mata bara a fadin Jiharsa

‘Yan Sanda sun kama wanda ya hallaka ‘Danuwansa saboda IPhone 11 a Anambra
Samfurin wata sabuwar wayar IPhone 11 da aka yayi
Asali: UGC

Oriental Times ta ce da ya ke bada labarin yadda ya kashe ‘Danuwansa, ya bayyana cewa shayin bera ya sa wa ‘Danuwan na sa, shi kuma ya ci ya mutu.

Paul ya ke cewa ya yi amfani da wannan maganin kashe kwari ne a kan ‘Danuwansa a cikin kalacinsa na safe, ya na cin abincin bai ko kara shurawa ba.

Ko da hukuma ta na shirin gurfanar da shi a gaban kotu da zargin aikata kisan kai, rahotanni sun bayyana cewa Mahaifiyarsu ta shiga cikin maganar.

Jaridar ta ce tsohuwar Yaran ta na rokon ‘Yan Sanda su saki Paul domin a halin yanzu shi kadai ne ‘Dan da ta ke da shi a Duniya bayan mutuwar wancan.

Ana saida sabuwar wannan waya ta IPhone 11 kirar Apple a kan kudin Najeriya akalla N300, 000 a kasuwa. Wannan waya ta na cikin wanda ake yayi a yanzu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng