An yi ram da mutum 3 wadanda su ka nemi su yi garkuwa da Sarkin Potiskum

An yi ram da mutum 3 wadanda su ka nemi su yi garkuwa da Sarkin Potiskum

Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta bada sanarwar kama wasu karin mutane da ake zargi akwai hannunsu wajen yunkurin sace Mai Martaba Sarkin Potiskum.

Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan kasa, Frank Mba, ya bayyana cewa ana zargin wadanda aka kama da laifin kai wa Matafiya hari a kan manyan hanyoyin Arewa.

DCP Mba ya bayyana cewa ana zargin wadannan mutum uku da laifin kokarin yin garkuwa da Mai martaba Sarkin Potiskum, har su ka kashe ‘Yan Sandansa.

A cewar Mba, ‘Yan kungiyar Ansaru da ke hannun ‘Yan Sanda a yanzu sun kai mutane takwas.

“Bayan harin da Jami’an ‘Yan Sanda su ka kai a sansanin ‘Yan ta’addan Ansaru da ke cikin dajin Kaduru, a Birnin Gwari, an sake kama wasu ‘Yan kungiyar.”

Mba ya cigaba da cewa: “wadanda aka cafke su ne: Munkailu Liman Isah watau Babban Driver Abdullahi Saminu watau Danmunafiki da kuma Aminu Usman.

KU KARANTA: 'Dan Sanda Abba Kyari ya samu sarauta a kasar Borno

An yi ram da mutum 3 wadanda su ka nemi su yi garkuwa da Sarkin Potiskum
Kwanakin baya aka yi kokarin sace Sarkin Potiskum a Kaduna
Asali: UGC

Kakakin ‘Yan Sandan wanda ya ke kan matsayi na Mataimakin Kwamishina, ya bada shekarun wadanda aka kama da 32, 21, da kuma 22, Dukkansu Mazaje ne 'Yan Yankin Arewa.

“Binciken da aka soma ya nuna cewa wadanda aka kama su na da hannu wajen yunkurin garkuwa da Sarkin Potiskum, wanda hakan ya jawo mummunan kisan Dogaransa.”

“Da su aka rika sace Bayin Allah tare da kai wasu munanan hare-hare da-dama a kan Matafiya da Bayin Allah a kan hanyoyin Arewa maso Gabas da Arewa ta tsakiya.” Inji Mba.

“Abin takaicin shi ne bincike ya nuna cewa mutanen Gari musamman ‘Yan kasuwa su na taimakawa wadannan ‘Yan ta’adda ta hanyar huldar kasuwanci da su.”

Sufetan ‘Yan Sanda ya kara jaddada niyyarsa na kokarin kawo zaman lafiya a Yankunan.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel