Murabus: Hadimar Shugaban kasa ta maidawa Enyinnaya Abaribe martani

Murabus: Hadimar Shugaban kasa ta maidawa Enyinnaya Abaribe martani

Lauretta Onochie ta yi kaca-kaca da Sanata Enyinnaya Abaribe saboda kiran da ya yi na cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sauka daga kan mulki.

Sanatan ya yi wannan jawabi ne a sakamakon tabarbarewar da sha’anin tsaro ya yi. Lauretta Onochie ta na ganin cewa Enyinnaya Abaribe ya sauka daga layi.

Onochie wanda ta ke taimakawa shugaban kasa a kan harkokin yada labarai ta kafafen zamani ta bayyana cewa ba a Najeriya kadai ake fama da rashin tsaro ba.

“Lamarin tsaro abin kuka ne ko ina a Duniya har da Najeriya. Magana Abaribe na cewa ‘Yan Najeriya su jefe SU, ya fita daga layi, neman tada zaune tsaye ne.”

Hadimar shugaban kasar ta kira shugaban marasa rinjaye a majalisar dattawan Najeriyan da shashasha a martanin da ta maida masa ta shafinta na Tuwita jiya.

KU KARANTA: Shugaban kasa Buhari ya yi wa Abaribe raddi mai kaushi

Mai bada shawarar ta kuma kara cewa: "Ga masu jin maganarsa (Enyinnaya Abaribe), Najeriya ba Sanata Ike Ekweremadu ba ce. Ka da ku jarraba haka. Kul!”

Misis Onochie ba ta tsaya nan ba, ta ce dama ‘Dan takarar shugaban kasan PDP, Atiku Abubakar ya yi alkawarin za a ga kashe-kashe idan har Buhari ya zarce.

Amma duk da wadannan kalamai da Atiku Abubakar ya yi, babu wanda ya dauki duwatsu ye jefa sa. Duwatsu nawa shi Abaribe ya sa ya jefa sa a lokacin?

"Ka fara dauko dutse ka yi jifan, mu na jiranka." Inji Onochie.

Bayan wannan, Hadimar fadar shugaban kasar ta zargi Sanata Abaribe da hada-kai da shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, wajen kawowa Najeriya matsala.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel