Kuma dai: Kotu ta sake dage shari’ar shugaban yan Shia, Ibrahim Zakzaky

Kuma dai: Kotu ta sake dage shari’ar shugaban yan Shia, Ibrahim Zakzaky

Wata babbar kotun jahar Kaduna ta sake dage cigaba da sauraron shari’ar da ake fafatawa tsakanin gwamnatin jahar Kaduna a bangare daya da shugaban yan Shia, Ibrahim Zakzaky tare da matarsa Zeenat a bangare guda.

Channels TV ta ruwaito Alkalin kotun, mai sharia Gideon Kuradah ne ya bayyana haka a zaman kotun na ranar Alhamis, 6 ga watan Feburairu, inda yace ya dage zaman sauraron karar har zuwa ranar 24 da 25 na watan da muke ciki.

KU KARANTA: Akwai yiwuwar gwamnatocin kasashen waje na tallafa ma Boko Haram – Majalisa

Haka zalika a yayin zaman na ranar Alhamis, Kuradah ya yi gyaran fuska ga adadin mutanen da ake kara a gabansa daga hudu zuwa biyu domin a samu daman fara shari’ar Zakzaky da matarsa, sakamakon har yanzu ba’a kamo sauran mutane biyun ba.

Alkali Kuradah ya bada umarnin a kyale likitocin Zakzaky su samu daman duba lafiyarsa a kurkukun Kaduna, amma tare da sa idon shuwagabannin gidan yarin.

Sai dai lauyan Zakzaky, Femi Falana ya bayyana bacin ransa da yawan dage shari’ar, inda yace hakan na kawo matsala ga lafiyarsa da na matarsa, tare da tauye walwalarsu, duk da dai Zakzaky da matarsa basu samu halartar zaman kotun ba.

A gabanin zaman kotun, an hangi jami’an tsaro da dama sun mamaye duk hanyoyin da suke makwabtaka da kotun, haka zalika jami’an tsaro sun yi dafifi a cikin harbar kotun don hana aukuwar karya doka da oda daga bangaren yan Shia.

Gwamnatin jahar Kaduna na tuhumar Zakzaky da matarsa a kan laifuka guda 8 da suka danganci kisan kai, haramtaccen taro, shiga hakkin jama’a da dai sauransu, hakan tasa aka kamasu tun watan Disambar 2015 biyo bayan arangama tsakanin mabiyansu da Sojoji a Zaria.

A zaman kotun na baya, Alkali Kuradah ya umarci hukumar DSS ta mika Zakzaky ga kurkukun Kaduna domin lauyoyinsa su samu saukin ganawa da shi a duk lokacin da bukatar hakan ya taso.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel