Rundunar soji ta karrama hazikan sojoji 37 a arewa maso gabas

Rundunar soji ta karrama hazikan sojoji 37 a arewa maso gabas

Rundunar sojin Najeriya ta karrama jami’ai da sojojin Operation Lafiya Dole su 37 sakamakon hakazakarsu wajen yaki da ta’addanci a yankin arewa maso gabashin kasar.

Jagoran shirya labarai na rundunar sojin Najeriya, Kanal Aminu Iliya, ya bayyana hakan a wani jawabi a jiya Lahadi, 2 ga watan Fabrairu a Abuja.

Iliyasu ya bayyana cewa mahukunta na rundunar soji ce ta gani jami’ai da sojojin a nazarinta ka ayyukan dakarun karkashin operation lafiya dole.

Ya bayyana cewa an gano cewa jami’an sun zage damtse a filin daga inda suka nuna hazikanci, sanin kan aiki, jajircewa da kuma kwarewa wanda hakan ne ya basu damar samun wannan lambar yabo.

Rundunar soji ta karrama hazikan sojoji 37 a arewa maso gabas
Rundunar soji ta karrama hazikan sojoji 37 a arewa maso gabas
Asali: Depositphotos

A cewarsa, yayinda aka baiwa hazikan jami’ai wasikun yabo na musamman, sojoji a daya bangaren za su samu Karin girma zuwa makamai na gaba.

Shugaban hafsan soji, Laftanal Janar Tukur Buratai ya taya wadannan sojoji murna inda ya bukaci da su kara zage damtse wajen kawo karshen ta’addanci da dukkanin matsalolin tsaro da ke addabar kasar.

Iliyasu ya bayyana cewa daga cikin jami’an da aka karrama akwai Birgediya janar guda biyu, kanal daya, Laftanal kanal guda hudu, manjo biyu, kyaftin biyar da kuma Laftanal hudu.

Ya kara da cewa sojojin da aka karrama akwai sajan din ma’aikata, biyu, kofur shida, da Lance kofur uku da kuma sojoji masu zaman kansu takwas.

Ya lissafo jami’an a matsayin: Brig. Gen. Olufemi Oluyede, kwamandan Brigad 27; Brig. Gen. Ahmadu Mohammed, tsohon kwamandan Birgade 26 Gwoza; da Col. Mohammed Babayo, kwamandan babban sansanin soji, Benisheik.

Sauran sune; Lt. Col. Isah Yusuf, kwamnadan bataliya 158; Lt. Col. Abayomi Biobaku, kwamnadan bataliya 159; Lt. Col. Jerry Maigari, kwamandan bataliya 251 da Lt. Col. Tajudeen Lamidi, kwamandan bataliya 192.

Har ila yau akwai: Maj. Michael Ndubuisi, Army Headquarters Strike Group; Maj. Abdullahi Muhammad, 212 Battalion; da Capt. Emeka Chukwu, Headquarters Theatre Command.

KU KARANTA KUMA: Al’amarin tsaro a arewa maso gabas na kara tabarbarewa – Sanata Ndume

Sauran sun Capt. Audu Kure – 192 Battalion; Capt. Alhassan Abdulkadir – 192 Battalion; Capt. Festus Fatunberu – 212 Battalion da Capt. Haruna Dabai – Headquarter 7 Division.

Da Lt. Baba Mala, 3 Battalion (Main); Lt. Osazee Asemota, 144 Battalion; Lt. Jeremiah Abomchi, 212 Battalion and L.t Suleiman Kirikpo, bataliya 231.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel