Matar Aure Ta Sace Jariri bayan Kwashe Lokaci Tana Zabgawa Mijinta Karya

Matar Aure Ta Sace Jariri bayan Kwashe Lokaci Tana Zabgawa Mijinta Karya

  • Rundunar ’yan sandan Kebbi ta kama Khadija Ibrahim, ’yar shekara 19, bisa zargin satar jariri a Zuru tare da kai shi wajen mijinta
  • Khadija Ibrahim ta yi wa mahaifiyar jaririn alkawarin debo ruwan zafi, amma ta tsere da jaririn bayan haihuwarsa
  • ’Yan sanda sun kwato jaririn tare da mayar da shi ga mahaifiyarsa ta asali, yayin da ake ci gaba da binciken lamarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kebbi - Rundunar ’yan sandan jihar Kebbi ta kama wata mata mai suna Khadija Ibrahim, ’yar shekara 19, bisa zargin satar jariri a jihar Kebbi.

'Yan sandan sun cafke matar ne a karamar hukumar Zuru bayan ta sace jaririn tare da gabatar da shi ga mijinta a matsayin ɗansu.

An cafke barauniyar jariri a Kebbi
Taswirar jihar Kebbi, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Jaridar The Punch ta ce hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, SP Bashir Usman, ya fitar ranar Lahadi, 16 ga watan Agustan 2026.

Kara karanta wannan

Ana kaɗa ƙuri'a a Osun, ƴan sanda sun faɗi tanadinsu kan zaben Bauchi

Sanarwar ta ce an kama Khadija, mazauniyar Rikoto a Karamar Hukumar Zuru, ranar 14 ga Agusta, 2026, bayan ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin da ya faru ranar 23 ga Yuli, 2025.

A cewar ’yan sandan, ana zargin matar ta sace jaririn ne jim kaɗan bayan mahaifiyarsa ta asali, Fatima Muhammad, ta haife shi, jaridar Vanguard ta kawo labarin.

Yadda aka sace jaririn

Rundunar ta ce Khadija ta yi kamar tana son taimaka wa sabuwar mahaifiyar, inda ta yi tayin zuwa debo mata ruwan zafi, amma ana zargin ta yi amfani da wannan damar ta gudu da jaririn.

“Binciken farko ya nuna cewa ana zargin wadda ake tuhuma ta fuskanci matsin lamba daga maganganun mutane saboda har yanzu ba ta samu haihuwa ba, yayin da wasu daga cikin takwarorinta suka riga suka haihu,” in ji sanarwar.

’Yan sandan sun kuma ce Khadija ta yaudari mijinta na tsawon kimanin watanni tara, inda ta sa shi ya yi imanin cewa tana da ciki.

Kara karanta wannan

Maganin mallaka: Matashin da ya birne Kur’ani da wasu kayan tsubbu ya shigo hannu

“Bayan haihuwar jaririn Fatima Muhammad, ana zargin ta ɗauki yaron ta kai wa mijinta a matsayin ɗansu,” in ji sanarwar.

An mayar da jaririn ga mahaifiyarsa

Rundunar ta ce daga baya an samu nasarar kwato jaririn tare da mayar da shi ga mahaifiyarsa ta asali.

Khadija na ci gaba da kasancewa a hannun ’yan sanda, kuma ana sa ran gurfanar da ita a gaban kotu bayan kammala bincike.

Kwamishinan ’yan sandan Jihar Kebbi, CP Umar Hadejia, ya yaba wa jami’an da suka gudanar da aikin bisa ƙwazo da kwarewarsu wajen kwato jaririn da kama wadda ake zargi.

Ya kuma tabbatar wa mazauna jihar cewa rundunar za ta ci gaba da kare yara tare da tabbatar da cewa duk wanda aka samu da laifin aikata laifi ya fuskanci hukuncin da ya dace.

An cafke barauniyar jariri a Kebbi
Shugaban rundunar 'yan sandan Najeriya, Olatunji Disu Hoto: @PoliceNG
Source: Facebook

An ceto jaririn da aka sace

A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar ’yan sandan jihar Benue ta tabbatar da ceto wani jariri da aka yi zargin sace shi sa’o’i kadan bayan haihuwarsa a wani asibiti da ke karamar hukumar Gboko ta jihar.

An haifi jaririn ne a safiyar ranar 11 ga watan Agusta, 2026 inda rahotanni suka ce an dauke shi daga wajen mahaifiyarsa jim kadan bayan haihuwarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng