Haihuwa: Ban son jin wannan maganar – Inji Mahaifin Leah Sharibu
Rade-radi sun fara yawo cewa wata karamar yarinya Leah Sharibu, da ke tsare a hannun Boko Haram ta haihu bayan samun juna biyu da ‘Yan ta’adda.
Wannan mummunan labari ya soma yawo ne a karshen makon nan. Ana zargin an yi wa wannan Kiristar auren dole da wani shugaban Boko Haram.
Jama’a da dama su na ta magana game da wannan mugun aiki na Sojojin Boko Haram. ‘Yan jarida sun samu sun yi magana da Mahaifinta a jiya Ranar Asabar.
Kamar yadda mu ka samu labari daga Jaridar Vanguard, Mahaifin wannan Baiwar Allah, Mista Nathan Sharibu, ya yi watsi da wannan mugun labari.
Nathan Sharibu ya nuna cewa sam bai yarda ‘Diyarsa ta haihu da ‘Yan ta’addan ba. Shekara fiye da guda kenan yanzu da sace Leah Sharibu tare da wasu.
KU KARANTA: Leah Sharibu ta haifawa Dakaren Boko Haram yaro a tsare

Asali: Depositphotos
“Ban ji wannan labari ba, kuma ba na son jin irin wannan labarin” a cikin fushi, Sharibu ya fadawa ‘Yan jarida wannan a Ranar 26 ga Junairun 2020.
‘Yan Boko Haram sun saki sauran ‘Yan matan makarantar da su ka dauke tare da ita, amma su ka cigaba da rike ta saboda ta ki karbar musulunci.
Kwanaki Iyayeyen wannan Yarinya su ka fito su na alfahari da yadda ta ki yin watsi da addinta duk da ta shiga hannun ‘Yan ta’addan Boko Haram.
Hakan na zuwa ne bayan rade-radin da aka rika yi na cewa Budurwar ta mutu. Mahaifiyarta, Rebecca Sharibu, ta ce ta na sa ran cewa Leah na nan.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi
https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng