Abubuwa 10 da Suka Bayar da Mamaki a Zaben Gwamnan Osun

Abubuwa 10 da Suka Bayar da Mamaki a Zaben Gwamnan Osun

  • Gwamna Ademola Adeleke ya samu tazarce bayan ya lashe zaben gwamnan jihar Osun da aka gudanar a ranar Asabar, 15 ga watan Agustan 2026
  • Ademola Adeleke ya samu nasara ne bayan ya lallasa abokin hamayyarsa na jam'iyyar APC, Bola Oyebamiji, bayan ya ba shi tazarar kuri'u fiye da 60,000
  • Zaben gwamnan na jihar Osun ya zo da abubuwan ban mamaki wadanda suka hada da rashin nasarar Rauf Aregbesola a rumfar zabesa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Osun - Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta sanar da Gwamna Ademola Adeleke a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Osun.

Gwamna Adeleke ya samu nasarar ne bayan ya samu kuri'u 511,067, inda ya doke babban abokin hamayyarsa, Bola Oyebamiji na APC, wanda ya samu kuri’u 444,815.

Kara karanta wannan

Bayan tumurmusa shi a zabe, Gwamna Adeleke ya aika sako ga dan takarar APC

Adeleke ya samu tazarce a zaben Osun
Dan takarar ADC, Najaam Salaam, dan takarar APC, Bola Oyebamiji da Gwamna Ademola Adeleke Hoto: Dr Najaam Folasayo Salaam, Bola Oyebamiji, Sen Ademola Adeleke
Source: Facebook

Legit Hausa ta rahoto cewa an sanar da sakamakon zaben ne da safiyar ranar Lahadi, 16 ga watan Agustan shekarar 2027.

Abubuwan ban mamaki a zaben gwamnan Osun

Zaben na gwamnan Osun ya zo da abubuwan mamaki da dama ciki har da ADC mai adawa ba ta yi wani katabus ba.

Ga jerin wasu abubuwan ban mamaki a zaben:

1. Fitowar masu kada kuri'a

Wani abin da ya dauki hankali kan zaben gwamnan jihar Osun shi ne yadda mutane suka fito domin kada kuri'unsu.

Mutane da dama sun fito tun da wuri domin kada kuri'unsu a zaben wanda aka gudanar a ranar Asabar, 15 ga watan Agustan 2026.

2. Rashin nasarar APC

Duk da karfin mulki a matakin tarayya, jam'iyyar APC ta gaza samun nasara a zaben gwamnan jihar Osun

APC ta tura manyan 'yan siyasa da suka hada da gwamnoni domin zaben na Osun, amma duk da haka, Bola Oyebamiji bai samu nasarar kayar da Ademola Adeleke ba.

Kara karanta wannan

2027: NDC ta daura damara, za a yi wa gwamnan Kano abin da Accord ta yi a Osun

3. Faduwar Aregbesola

Tsohon gwamnan jihar Osun kuma sakataren jam'iyyar ADC na kasa bai yi katabus ba a zaben, inda ya kasa lashe rumfar zabensa.

Jam'iyyar APC ta lashe a rumfar zaben Aregbesola inda dan takararta Bola Oyebamiji ya samu kuri'u 256, Gwamna Adeleke na Accord ya samu kuri'u 43 yayin da dan takarar ADC, Najaam Salaam ya samu kuri'u 13 kacal, cewar rahoton Premium Times.

4. An yi amfani da janareta domin ci gaba da kada kuri'a

Wani abin mamaki da ya faru shi ne a rumfar Bola Oyebamiji da ke Ikire I, karamar hukumar Irewole, inda aka ci gaba kada kuri'a ta ci gaba har bayan magariba.

Lamarin ya faru ne bayan da duhu ya fara yi ba a kammala kada kuri'a ba, wanda hakan ya sanya jami'ai suka shirya amfani da janareta domin samar da haske don aikin ya ci gaba.

5. An yi harbe-harbe a cibiyar tattara sakamako

An ji karar bindiga a harabar Union Baptist Primary School da ke Osogbo, inda aka kafa cibiyar tattara sakamakon Ataoja D Ward 4.

Kara karanta wannan

Adeleke: Abubuwa 7 da ya kamata ku sani game da wanda ya lashe zaben gwamnan Osun

Rahoton jaridar jaridar Vangarud ya nuna cewa harbe-harben ya faru tsakanin 9:15 zuwa 9:30 na daren ranar Asabar, 15 ga watan Agustan , lamarin da ya sa mutane suka gudu neman mafaka.

6. Rikici a rumfar zaben Najeem Salaam

An samu hargitsi bayan dan takarar ADC, Najeem Salaam, ya kada kuri'arsa tare da matarsa a Ejigbo.

Jami'an tsaronsa sun gaggauta tafiya da shi, yayin da jami'an INEC, masu sa ido da 'yan jarida suka gudu daga wurin.

7. An kama bakin haure 300

Rundunar 'yan sanda ta bayyana cewa ta cafke wasu mutane kusan 300 a gidan wani mai ruwa da tsaki a siyasa.

Jami'an tsaron na 'yan sanda sun bayyana cewa mutanen shigo da su aka yi daga makwabtan jihohi na Ekiti da Ondo.

8. Musayar yawun Faleke da Davido

Fitaccen mawaki Davido ya zargi James Faleke da matsa wa INEC lamba domin sauya sakamakon zabe.

Faleke ya musanta hakan, yana cewa ya je Osun ne kawai domin tallafa wa dan takarar APC. Daga baya, bayan Adeleke ya yi nasara, Faleke ya taya shi murna.

9. Tinubu ya taya Adeleke murna

Kara karanta wannan

Tirkashi: An gwabza tsakanin Davido da dan majalisa kan zaben gwamnan Osun

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kira Gwamna Ademola Adeleke domin taya shi murna tun kafin a sanar da sakamakon zabe a hukumance.

Wani jigo a jam'iyyar Accord kuma mai magana da yawun kwamitin yakin neman zaben Gwamna Adeleke, Pelumi Olajangbesi, ya tabbatar da cewa Shugaba Tinubu ya kira gwamnan tun cikin daren ranar Asabar.

Adeleke ya lashe zaben gwamnan Osun
Gwamna Ademola Adeleke tare da Davido Hoto: @AAdeleke01
Source: Twitter

10. Rashin katabus din ADC

Jam'iyyar ADC wadda ake yi wa kallon daya daga cikin manyan jam'iyyun adawa a Najeriya, ba ta haska ba a zaben gwamnan Osun.

Duk da kasancewar sakataren jam'iyyar na kasa kuma tsohon gwamnan jihar Osun, Rauf Aregbesola a cikinta, ADC ta kasa samun kuri'u 20,000 a zaben.

Gwamna Adeleke ya yi magana kan nasararsa

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, ya mika godiyarsa ga Shugaba Bola Tinubu bayan ya samu nasara a zaben gwamnan jihar.

Gwamna Ademola Adeleke ya bayyana sake zabensa a matsayin nasara ga dimokuraɗiyya da al’ummar Osun.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng