Gwamna Radda Ya Fadi Goma Ta Arziki da Tinubu Ya Yi wa Gwamnonin Jihohi
- Gwamnan Katsina, Dikko Radda, ya ce sauye-sauyen tattalin arzikin da Shugaba Bola Tinubu ya kawo na taimaka wa jihohi wajen gudanar da manyan ayyuka
- Radda ya ce gwamnatin Katsina ta aiwatar da ayyuka sama da Naira biliyan 30 ba tare da karɓar lamuni ba, yana mai cewa hakan ya nuna yadda ake cigaba
- Gwamnan ya kuma ce samun ’yancin kai na kuɗin ƙananan hukumomi na daga cikin sauye-sauyen da suka taimaka wa jihohi wajen sauke nauyin da ke kansu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Katsina – Gwamnan Katsina, Malam Dikko Radda, ya bayyana cewa sauye-sauyen tattalin arzikin da Bola Tinubu ya gabatar na taimaka wa gwamnatocin jihohi wajen gudanar da ayyukan ci gaba.
Radda ya bayyana hakan ne ranar Lahadi a wajen shirin tallafa wa malaman Islamiyya na Tinubu/Dikko 2027, da ƙaddamar da makaranta da kuma ƙaddamar da fitilun tituna 45 masu amfani da hasken rana a Katsina.

Source: Twitter
Punch ta rahoto gwamnan ya ce gwamnatinsa ta aiwatar da ayyuka da darajarsu ta haura Naira biliyan 30 ba tare da karɓar bashi ba.
Katsina ba ta karɓar bashi ba - Radda
Radda ya bayyana cewa a yanzu babu wani fanni da gwamnatin Katsina ke karɓar bashi domin aiwatar da wani aiki.
Ya ce gwamnatin jihar na iya biyan fansho da sauran nauyin da ke kanta ba tare da dogaro da lamuni ba.
“Yau babu wani fanni da muke karɓar bashi domin aiwatar da wani aiki guda a jihar Katsina. Muna biyan fansho tare da sauke nauyin da ke kanmu ga al’ummar Katsina.
“Yanayin ya bambanta a baya, lokacin da jihar ke dogaro da bashi wajen biyan albashin ma’aikata,”
In ji shi.
Gwamnan ya ce ya kamata a rika tantance shugabanni bisa la’akari da ayyukan da suka gudanar da kuma sakamakon da ake iya gani, maimakon kalaman siyasa ko labaran da ba su da tushe.

Kara karanta wannan
Mataimakin gwamna ya kawo ruɗani, ya ce yan bindiga sun kai hare hare ƙananan hukumomi 26
Maganar Aminu Masari
Tsohon gwamnan jihar Katsina, Aminu Masari, ya ce ya kamata shugabannin siyasa sun rika fifita jin daɗin jama’a da ci gaban al’umma.
Gwamnatin Katsina ta wallafa a Facebook cewa Masari ya ce duk wanda ya ƙi amincewa da nasarorin Shugaba Tinubu da Gwamna Radda yana yin abin da ya kira munafunci.
“Duk wanda ya yi watsi da nasarorin Shugaba Tinubu da Gwamna Radda akwai munafurci tattare da shi,”
In ji tsohon gwamnan.

Source: Facebook
Masari ya kuma yaba da yadda aka inganta hanyar Kaduna zuwa Abuja, yana mai cewa hakan na daga cikin alamun tasirin shugabanci mai inganci.
Za a samawa Tinubu kuri'u
A wani labarin, mun ruwaito cewa Shugaban wata tafiyar jam'iyyar APC ya bayyana kwarin gwiwar cewa APC za ta samu aƙalla kuri’u miliyan ɗaya ga Shugaba Bola Tinubu a jihar Ondo a zaɓen 2027.
Ijabiyi ya bayyana hakan ne yayin da yake magana kan shirin ƙungiyar na ƙara wayar da kan jama’a da kuma tura magoya baya zuwa matakin ƙasa da ƙasa domin tabbatar da nasarar Tinubu.
Ya ce ƙungiyar ta kafa wannan tsari ne musamman domin tabbatar da nasarar Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027, duk da rikice-rikicen cikin gida da suka dabaibaye reshen APC a jihar Ondo.
Asali: Legit.ng
