Sojoji Sun Ɗana Tarko, An Daƙile Harin Garkuwa da Mutane a Zamfara
- Sojojin Operation Fansan Yamma sun kubutar da wasu bayin Allah, daga cikinsu har da jariri, daga hannun ’yan bindiga da suka kai wani hari Zamfara
- Fitinannun yan bindigan sun buɗe wa motocin da ke wucewa wuta a wata gonar gero, lamarin da ya jikkata mata biyu a yunkurin da ake na guduwa da su
- Amma dakarun sun yi kwanta-kwanta, sun mayar da martani mai zafi wanda ya firgita yan bindigar tare da dakile mummunan harin da aka kai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Zamfara – Sojojin rundunar hadin gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation Fansan Yamma, sun dakile wani yunkurin yin garkuwa da dimbin fararen hula a kauyen Unguwar Rogo da ke ƙaramar hukumar Kaura Namoda a jihar Zamfara.
Sojojin sun kuma kubutar da fararen hula tara, daga ciki har da wani jariri, bayan ’yan bindiga sun kutsa cikin yankin tare da kai wa mutanen da ke tafiya a wata hanya ta cikin gida hari.

Source: Facebook
Jaridar Punch ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne ranar Lahadi, 16 ga Agusta, 2026, bayan rundunar ta samu kiran gaggawa cewa ’yan ta’adda sun mamaye al’ummar tare da kai hari kan fararen hula.
Sojoji sun dakile hari a Zamfara
Jaridar Vanguard ta kawo labarin cewa a cikin wata sanarwa da jami’in yaɗa labarai na rundunar JTF na Arewa maso Yamma na Operation Fansan Yamma, Laftanar Kanal Aliyu Danja, ya ce ana zargin wani fitaccen ɗan ta’adda mai suna Mallam Shuaibu ne ya jagoranci harin.
Danja ya ce bayanan farko sun nuna cewa wataƙila harin ya kasance ramuwar gayya ne kan kama wasu mutane da ake zargi da taimaka wa ƙungiyar ’yan bindiga.
Ya bayyana cewa sojoji sun taɓa cafke waɗanda ake zargin a lokacin da suke ƙoƙarin samo babura da man fetur mai domin ci gaba da ayyukan ta'addancinsu.
An jikkata mata a Zamfara
A cewar Danja, daga bisani ’yan bindigan sun ɓuya a cikin gonar gero da ke gefen hanyar, inda suka buɗe wa motocin da ke wucewa wuta da nufin yin garkuwa da mutanen.

Source: Facebook
Ya ce:
“’Yan ta’addan sun ɓuya a cikin gonar gero da ke gefen hanyar, inda suka buɗe wa motocin da ke wucewa wuta, lamarin da ya sa wasu direbobi suka kauce hanya."
Ya ce bayan samun kiran gaggawa, sojojin Sector 2 sun isa wurin cikin gaggawa tare da tunkarar ’yan bindigan, lamarin da ya tilasta musu tserewa zuwa dajin da ke kusa.
Danja ya ƙara da cewa sojojin sun samu nasarar kubutar da fararen hula tara da harin ya rutsa da su. Ya kuma bayyana cewa mata biyu sun samu raunukan harbin bindiga a lokacin harin, kuma an garzaya da su asibiti.
Sojoji sun kashe yan bindiga
A baya, mun kawo labarin cewa rundunar Sojin Najeriya ta ce dakarunta sun ceto mutane 23 da aka yi garkuwa da su, tare da hallaka ’yan ta’adda 19 cikin sa’o’i 24 a sassa daban-daban na Najeriya.
A Zamfara, Operation Fansan Yamma ya ceto mutane 18 da ’yan ta’adda suka yi garkuwa da su a gidajensu, bayan dakarun sun kai farmaki domin fatattakar yan bindigan da suka kai wadannan hare-hare.
A Borno, Operation Hadin Kai ya ceto mutane biyar da suka tsere daga sansanin ’yan ta’adda, yayin da sojoji suka kwato makamai a Enugu da sauran sassan Najeriya a yakin da ake yi da ta'addanci
Asali: Legit.ng

