Sojoji Sun Gano Dandazon 'Yan Bindiga da Tsakar Rana, Suna Shirin Afkawa Katsina

Sojoji Sun Gano Dandazon 'Yan Bindiga da Tsakar Rana, Suna Shirin Afkawa Katsina

  • Sojojin Birged na 17 na Rundunar Sojin Najeriya sun hango taron ’yan bindiga da ke shirin kai hari karamar hukumar Charanchi ta Jihar Katsina
  • Rundunar ta samu kiran gaggawa da 11.20 na safe, inda aka sanar da cewa wasu da ake zargin ’yan bindiga sun taru a kusa da kauyen Kaddanya
  • Sojojin sun gudanar da sintiri mai razana zuciyar masu aikata laifi tare da mamaye yankin bayan sun dauki mataki a kan dandazon yan bindigar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Katsina – Sojojin rundunar sojin Najeriya sun dakile wani shirin kai hari da wasu da ake zargin ’yan bindiga ne suka shirya a karamar hukumar Charanchi ta Jihar Katsina.

An dakile harin ne bayan rundunar ta samu kiran gaggawa da kusan 11.20 na safe ranar 9 ga Agusta, 2026, inda aka sanar da cewa wasu da ake zargin ’yan bindiga sun taru a kusa da kauyen Kaddanya da ke yankin.

Kara karanta wannan

Sojoji sun ragargaji 'yan ta'adda, an kashe fiye da 65 yayin da aka ceto mutane 360

Dakaru sun tarwatsa yan bindiga a Katsina
Wasu daga cikin yan bindiga, dakarun Najeriya suna murna a yayin aiki Hoto: @ZazazOlaMakama
Source: Twitter

Zagazola Makama ya wallafa a shafin X cewa wani rahoton tsaro ya ce sojojin da ke sansanin FOB Radda sun gaggauta mayar da martani bayan kiran gaggawar, inda suka tattara dakarunsu tare da nufar wurin da aka samu rahoton.

Sojoji sun firgita 'yan bindiga

Sojojin sun yi aiki tare da jami’an rundunar yan sandan Najeriya daga Kankia da Charanchi, da kuma jami’an tsaron Katsina, inda suka yi nasarar dakile shirin ’yan bindigan na kai hari.

An kuma ci gaba da sinitiri don hana yan bindiga dawowa yankin Katsina
Taswirar jihar Katsina da ke fama da matsalar yan bindiga Hoto: Legit.ng
Source: Original

Bayan kammala aikin, sojojin sun ci gaba da gudanar da sintiri mai tare da mamaye yankin baki daya domin hana wadanda ake zargin ’yan bindiga ne samun damar yin wani yunkuri.

Rhotanni sun kara da cewa matakin na daga cikin kokarin rundunar na takaita ayyukan ’yan ta’adda da kuma kare al’ummomin da ke yankin.

An jinjinawa sojoji a Katsina

An fara yabon sojojin Najeriya game da yadda suka yi gaggawar tarwatsa yan bindiga da ke shirin kai wa jama;ar Katsina hari bai gaira ba dalili.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun tare matafiya, sun budewa jama'a wuta

Wasu daga cikin mabiya shafin na ganin hakan zai taimaka wajen kare rayuka, amma akwai bukatar a kara hada kafi da karfe da kasar Amurka.

@JainKiama55673 ya ce:

'Yana da kyau sojojinmu sun dakile wannan harin a Katsina! Amma ku yi tunanin irin yadda za mu kara karfi idan muka samu taimako daga Amurka da sauran kasashe. Idan muka hada gwiwa da kasashen Yamma wajen horaswa, za mu iya mayar da hankali kan abubuwan da suka fi muhimmanci a gare mu."

Sojoji sun hallaka hatsabibin 'dan bindiga

A wani labarin, kun ji cewa rundunar DSS tare da jami'an tsaron sa kai sun yi nasarar hallaka kasrugumin jagoran 'yan bindiga Idi Abasu Aiki bayan wata arangama a jihar Katsina.

Rahotanni sun ce fiye da 'yan bindiga 200 ne suka kai hari Guga da nufin ramuwar gayya kan al'ummomin da ke taimaka wa masu tsaron sa-kai wajen wanzar da zaman lafiya a jihar.

Jami'an sun kuma yi nasarar kwato makamai da sauran kayayyaki da 'yan bindigar suka bari, amma duk da nasarar an samu asarar rayukan zaratan ma'aikata da suka rasu a fagen fama

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng