Mutane Sun Mutu da Gine Gine 2 Suka Rufta kan Daliban Islamiyya da Ma'aikata a Kano
- Mutane biyar, ciki har da ma’aikatan gini huɗu da ɗalibar makarantar Islamiyya, sun mutu sakamakon ruftawar wasu gine-gine a Kano
- Rahoto ya nuna cewa lamarin ya faru ne a Gaida da ke ƙaramar hukumar Kumbotso da Kurna a ƙaramar hukumar Fagge ranar Asabar
- Ma’aikatan hukumar kashe gobara sun ceto wasu mutane 10 da hatsarin ya rutsa da su, amma biyar sun mutu daga baya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Mutane biyar, ciki har da leburori huɗu da ɗalibin makarantar Islamiyya, sun mutu a wasu gine-gine biyu da suka ruguje a jihar Kano.
Hatsarin ruftawar gine-ginen ya faru ne ranar Asabar da ta wuce a Gaida da ke ƙaramar hukumar Kumbotso da Kurna da ke ƙaramar hukumar Fagge ta jihar.

Source: Original
Leadership ta ruwaito cews jami’in hulɗa da jama’a na Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, Saminu Yusif, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi.

Kara karanta wannan
Abin tausayi: Hatsarin jirgi ya rutsa da manoma a hanyar zuwa gonakinsu a Najeriya
Gini ya lashe mutane 4 a Kano
Yusif ya ce hatsarin farko ya faru da misalin ƙarfe 2.34 na rana a Gaida, kusa da gidsn mai na Salbas, inda wani ginin da ake ginawa wanda bai kammala ba ya ruguje kan ma’aikata shida.
Ya ce an ceto biyu daga cikin ma’aikatan, Muhammad Hassan mai shekaru 17 da Khalid Abubakar mai shekaru 19, da ransu.
Sai dai ma’aikatan kashe gobarar sun fito da wasu huɗu daga cikin ginin a sume, kuma daga baya aka tabbatar da mutuwarsu.
An bayyana sunayen mamatan da Sunusi Surajo mai shekaru 18, Bashir Ibrahim mai shekaru 20, Ibrahim Ibrahim mai shekaru 25 da Abubakar mai shekaru 30.
A cewarsa, an kwashe dukkan mutanen shida zuwa Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad, inda aka miƙa su ga ‘yan sanda.
Ɗalibar Islamiyya ta mutu
Yusif ya ce lamari na biyu ya faru ne bayan kusan mintuna shida a Kurna, a bayan makarantar firamare, inda wani ginin makarantar Islamiyya mai suna Khadija Idris Bala ya ruguje.
Ya ce ɗalibai tara ne abin ya shafa, inda aka ceto takwas da ransu, amma Khadija Muhammad mai shekaru 14, wadda aka ceto a sume, ta mutu daga baya.
An bayyana sunayen waɗanda suka tsira da Hassana Isah, Usaina Isah, Zulaihat M. Gambo, Nawara Yahaya, Nusaiba Isah, Hasiya Munir, Khadija Isah da Hadiza Haruna.
Kakakin hukumar kashe gobara ya ce an miƙa waɗanda lamarin ya rutsa da su ga shugaban makarantar, Muhammad Gambo Usman.

Source: Facebook
Ana binciken dalilin ruftawar gini
Hukumar Kashe Gobara ta ce ana ci gaba da binciken musabbabin rushewar gine-ginen biyu, kamar yadda Daily Post ta kawo.
Yusif ya buƙaci masu gine-gine, ‘yan kwangila da leburori su kiyaye dokokin tsaro da ƙa’idojin gini, musamman a lokacin damina, domin hana sake samun rushewar gine-gine da asarar rayuka.
Gini ya yi ajalin uwa da yaranta 2
A baya, kun ji wata mata mai shekara 35 da ’ya’yanta biyu sun mutu bayan wani gini da ake ginawa ya rufta kan gidansu a jihar Kaduna.
Mijin matar, Abubakar Abba Haruna, ya ce ba ya gida lokacin da lamarin ya faru, domin ya kwana a gidan dayar matarsa.
Asali: Legit.ng
