Shugaban Sojojin Najeriya
A jiya ne Shugaban Hafsun Sojin kasa a Najeriya, Laftana Janar Tukur Yusuf Buratai ya canzawa manyan Sojoji 6 wurin aiki. Wanda abin ya shafa sun hada da gidan GOC na 6, NDA, da MNJTF.
Wani bidiyo yana ta yawo a shafukan sada zumunta inda aka ga sojoji suna ta ladabtar da wani mutumi ta hanyar sanya shi yin wanka a cikin kwata saboda ya saci takalmi na kimanin naira dubu ashirin (N20,000) ya kuma sayar da shi...
Jihohin Katsina da Garin IGP sun samu kaso mai tsoka a aikin ‘Yan Sanda. Mafi yawan jihohin Kudancin kasar sun cutu kamar yadda mu ka fahimta.
Sai kwanan nan ne wani tsohon Soja ya yi magana game da kisan Dele Giwa da ya faru a 1986. Yanzu dai gaskiya ta fara fitowa kan wannan ‘Dan Jaridar da aka kashe lokacin Babangida ya na mulki.
Bakin yakin da ake yi tsakanin shugaban hukumar ‘yan sandan Najeriya ya ki mutuwa a halin yanzu. Labarai daga Punch na zuwa mana cewa an cigaba da rikici a gidan ‘Yan Sanda duk da sa bakin Shugaba Buhari.
Sanata Shehu Sani ya nemi Buhari ya sa baki a rikicin ‘Yan Sandan Najeriya inda daukar aiki ya hada Sufetan ‘Yan Sanda da Hukumar PSC fada wanda har gobe rikicin ya ki cinyewa.
Wasu manyan kwamandojin rundunar Sojin Najeriya dake yaki da yan ta’addan Boko Haram sun koka kan rashin ingantattun makamai na zamani da zasu taimaka musu wajen gamawa da mayakan na Boko Haram a yankin Arewa gabas.
A kalla sojin Najeriya 13 suka rasa rayukansu a kwanaki kadan da suka gabata. Sun rasa rayukansu a harin da 'yan Boko Haram me kaiwa rundunar sojin a gabas maso arewan, inji majiya daga rundunar. Maharan sunyi gaba da kayayyakin a
A jiya Alhamis ne 12 ga watan Satumbar nan matar shugaban kasar Najeriya Aisha Buhari, tayi kira ga hukumomin tsaro na kasar nan da su tura sojoji mata suyi yaki da matsalar tsaro a wasu jihohi na kasar nan...
Shugaban Sojojin Najeriya
Samu kari