An Kama Dan Bindiga Makare da Naira da Dalolin Amurka Yana Shirin Guduwa

An Kama Dan Bindiga Makare da Naira da Dalolin Amurka Yana Shirin Guduwa

  • Sojojin Runduna 82 da ke aiki tare da Jami’an DSS sun kama wani fitaccen kwamandan ƙungiyar masu garkuwa da mutane
  • Rahoto ya nuna cewa dakarun dojojin sun kuma kwato bindigogi kirar AK-47 guda huɗu da tarin harsasai daga maboyarsu
  • Bincike ya nuna cewa wanda aka kama yana da alaƙa da ayyukan satar mutane a Kudu maso Gabas da Arewa ta Tsakiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Enugu – Sojojin Runduna ta 82 tare da haɗin gwiwar jami’an Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS), sun samu gagarumar nasara wajen tarwatsa wata ƙungiyar masu garkuwa da mutane a jihar Enugu.

A yayin wani samame da aka gudanar bisa bayanan sirri a yankin Gariki General Area na jihar, sojojin sun kama wani fitaccen kwamandan ƙungiyar masu garkuwa da mutane tare da kwato makamai da alburusai daga maboyarsu.

Kara karanta wannan

Nasara daga Allah: Sojoji da yan sanda sun rutsa yan bindiga fiye da 200 ta sama da ƙasa

Dan bindigan da aka kama a Enugu
Dan bindiga tare da kudin da aka kama shi da su. Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Facebook

A sakon da sojojin suka wallafa a Facebook, sun ce an gudanar da aikin ne bayan an shafe lokaci ana ƙoƙarin tarwatsa ƙungiyar da ake zargi da yin garkuwa da mutane biyu a ƙaramar hukumar Udi ta jihar Enugu a ranar 2 ga Agusta 2026.

An kama dan bindiga a Enugu

Bayan samun bayanan sirrin, sojojin sun ƙara tsaurara farautar kwamandan, inda daga bisani suka gano shi, suka tare shi tare da kama shi yayin da yake ƙoƙarin tserewa daga jihar Enugu.

Binciken farko ya nuna cewa wanda aka kama yana da alaƙa da wasu hare-haren garkuwa da mutane da aka gudanar a yankunan Kudu maso Gabas da Arewa ta Tsakiya.

Punch ta rahoto cewa daga cikin abubuwan da aka kwato daga hannunsa akwai dala 1,000 na Amurka, tsabar kuɗi N785,900 da wasu kayayyakin da ake zargin suna da alaƙa da aikata laifuka.

An kwato AK-47 da harsasai 133

Kara karanta wannan

Sojoji sun gano dandazon 'yan bindiga da tsakar rana, suna shirin afkawa Katsina

Ƙarin bayanan sirri da aka samu daga waɗanda aka kama sun kai sojojin zuwa dajin Umuchingu Ujenike, inda ake zargin mambobin ƙungiyar sun ɓoye makamansu.

A yayin wani samame na bibiyar bayanan, sojojin sun kwato bindigogi kirar AK-47 guda huɗu, jakar harsashin AK-47 guda bakwai da wasu harsasai 133.

Rundunar ta ce nasarorin da aka samu sun ƙara nuna tasirin ayyukan haɗin gwiwa da ake gudanarwa bisa bayanan sirri wajen tarwatsa ƙungiyoyin masu aikata manyan laifuffuka.

Sojoji da wa wanda aka kama
Sojojin Najeriya bayan kama dan bindiga a Enugu. Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Facebook

Kwamandan ƙungiyar da aka kama yana hannun jami’an tsaro, inda ake ci gaba da yi masa tambayoyi domin samun ƙarin bayanan da za su taimaka wajen kama sauran mambobin ƙungiyar da masu haɗin gwiwarsu.

Rundunar, tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro, ta ce za ta ci gaba da gudanar da ayyukan leƙen asiri da samame kan masu aikata laifi a yankin Kudu maso Gabas.

An nemi kawar da 'yan bindiga

A wani labarin, mun ruwaito cewa Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yi kira ga Rundunar Sojin Najeriya da ta kawar da ‘yan bindiga da ke ci gaba da yin barazana ga rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar.

Kara karanta wannan

Ana shirin 2027, an gano bindigogi 399 da aka yi shirin kawowa Najeriya

Gwamnan ya yi wannan kiran ne ranar Juma’a yayin wata ziyara ba tare da sanarwa ba da ya kai sansanin sojoji da ke Yauri, inda ya yaba wa sojojin bisa jarumtaka da jajircewarsu wajen gudanar da ayyukansu.

Gwamna Idris ya sake jaddada aniyar gwamnatinsa na bai wa hukumomin tsaro dukkan goyon bayan da suke buƙata,wajen yaki da masu garkuwa da mutane.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng