An kama babban sojan Najeriya da ya gudu a kasar Benin

An kama babban sojan Najeriya da ya gudu a kasar Benin

Wani babban jami'in rundunar sojin Najeriya, Manjo Akeen Oseni, da kotun sojoji ta yanke wa hukuncin dauri amma kuma ya sulale daga harabar kotu ya gudu, ya shiga hannu.

An kama Manjo Oseni, wanda ya kasance daya cikin sojoji 10 da kotun soji ta musamman ta yanke wa hukuncin daurin shekaru 10, a filin jirage na Koton, babban birnin kasar Benin, da misalin karfe 2:00 na rana.

A ranar Juma’a, 7 ga watan Fabrairu ne rundunar sojin Najeriya ta yankewa wasu sojoji uku hukuncin zaman gidan yari na shekaru 10 a kan laifin kisan kai.

Sojojin da aka yankewa hukuncin sun hada da Manjo Akeem Oseni, manjo Ogbemudia Osawe da Laftanal Nuhu Dogari, kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.

An kama babban sojan Najeriya da ya gudu a kasar Benin
Manjo Akeem Oseni
Asali: Twitter

An kama sojojin ne da laifin azabtar da wani Collins Benjamin, soja mai mukamin 'lance corporal' wanda hakan yayi sanadin mutuwarsa.

DUBA WANNAN: Abinda yasa kawo karshen kungiyar Boko Haram ya yi wuya - Buratai

A ranar Litinin ne kafafen yada labarai suka rawaito cewa Oseni ya nemi izinin cewa zai yi amfani da bandaki bayan kotun ta karanta hukuncin da ta yanke a kansu, amma sai kawai ya sulale ya gudu.

Bayan an gano cewar ya gudu ne sai rundunar soji ta bayar da sanarwa ga duk cibiyoyinta da sansani a kan su kama Manjo Oseni a duk inda aka gan shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel