Tinubu da Wadanda Suka Agaji Jam'iyyar Accord Ta Yi Galaba a Zaben Jihar Osun
Osun - Idan abubuwa suka tafi a haka, Ademola Adeleke zai cigaba da mulkar jihar Osun a matsayin gwamna har zuwa 2030.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Gwamnan ya yi nasara da tazarar kuri’u 60, 000 a zaben da aka yi a ranar 15 ga Agusta 2026.

Source: Twitter
Wadanda suka ba gwamna nasara a Osun
Ademola Adeleke ya ga bayan Asiwaju Munir Bola Oyebamiji da Najeem F. Salaam na APC da ADC da wasu ‘yan takara sama da 10.
Rahoton nan ya yi kokarin duba wasu mutanen da kai-tsaye ko kuma a kaikaice suka tallafa wajen samun nasarar jam’iyyar Accord.
1. Ademola Adeleke
Rahotanni dauke da bayanin yadda ayyuka da farin jinin Gwamna Ademola Adeleke suka yi sanadiyyar yin galaba a kan jam’iyyar APC.
Duk da ba a san jam’iyyar Accord ba, gwamnan ya yi abin da ya yi har ta kai shi ga samun nasara, yanzu yana kan hanyar zarcewa a ofis.
A shekaru kusan hudu da ya shafe a ofis, Imole zai iya nuna ayyukan da zai yi kamfe da su a Osun.
2. Bola Tinubu
Gabanin zabe, an ji labari shugaban kasa ya gana da manyan APC da ya samu labarin akwai rashin jituwa tsakanin ‘ya ‘yan jam’iyyarsa a Osun.
Wannan kokari da Bola Tinubu ya yi wa APC bai sa ya hana a yi adalci ba, kuma kafin nan ya yi umarni EFCC ta bude asusun gwamnatin Osun.
Ana ganin goyon bayan da Adeleke zai ba Tinubu a zaben 2027 ya jawo shugaban kasa ya kira gwamna tun kafin a kai ga sanar da nasararsa.
3. Iyiola Omisore
Jaridu da yawa sun rahoto yadda jam’iyyar Accord ta yi galaba a kan APC har a rumfar da Iyiola Omisore yake kada kuri’arsa a yankin Odo-Otin.
Amma a zahirin gaskiya, tuni The Guardian ta rahoto cewa yaran Sanata Omisore za su yi wa Adeleke da jam’iyyarsa aiki a zaben nan na 2026.
Watakila tun da aka hana shi da wasu neman takara a jam’iyyar, ya yi niyyar kada ‘dan takarar APC.
4. David Adeleke
An yi ta yin sharhi game da kokarin da David Adeleke ya yi domin kawunsa ya koma kan karaga, ya yi fito na fito da manyan ‘yan APC a dandalin X.
Baya ga tallata gwamnatin Adeleke wajen kamfe, mawakin ya caccaki masu taba gwamna kuma ya tsaya tsayin-daka wajen hana magudi ranar Asabar.
Babu mamaki nan gaba a ga ana cusa fitattun taurari irinsa wajen yakin cin zabe a Najeriya.
5. Jam’iyyar Accord
Jam’iyyar Accord da ta karbi Mai girma Adeleke lokacin da ya watsar da tafiyar PDP a karshen shekar 2025 za ta shiga cikin wannan sahu.
Hadimin Muhammadu Buhari, Tolu Ogunlesi a X ya kawo labarin yadda ‘yan APC suka hana gwamnan shiga cikinsu da ya canza gida.
Ko a bara da ya nemi ya koma APC, irin haka aka nuna masa a karshe Accord ta karbe shi.
Tarihin gidan Adeleke a siyasa
Kafin Gwamna mai rawa kamar yadda ake kiransa, kun ji labarin wasu ‘yan zuri’ar Adeleke da suka yi suna a siyasa a shekarun da suka wuce.
Mahaifinsu, Raji Ayoola Adeleke ya fara siyasa ne tun zamanin Shehu Shagari kafin ‘ya ‘yansa biyu su zama gwamnoni a Osun da tsohuwar Oyo.
Marigayi Isiaka Adetunji Adeleke shi ne gwamnan jihar Osun na farko wanda kuma ya zama sanata mai wakiltar Osun ta yamma har sau biyu.
Asali: Legit.ng


