Dalibai 4 na Makarantar Haddar Alkur'ani Sun Mutu Lokaci Guda a Jihar Kano, An Gano Dalili

Dalibai 4 na Makarantar Haddar Alkur'ani Sun Mutu Lokaci Guda a Jihar Kano, An Gano Dalili

  • Almajirai huɗu sun mutu bayan rahotanni sun ce sun ci abincin da ake zargin ya gurɓata a ƙaramar hukumar Ungogo ta Jihar Kano
  • Rahoto ya nuna cewa almajiran sun mutu ne a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano a daren Lahadi, 16 ga Agusta, 2026
  • Wannan lamari dai ya tada hankulan jama'a, sai dai har yanzu ba a bayyana kalar abincin da suka ci har ya yi ajalinsu ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Daliban makarantar koyon karatun Alkur'ani, wacce aka fi sani da Tssngaya, sun mutu bayan rahotanni sun ce sun ci abincin da ake zargin ya gurɓata fa guba a ƙaramar hukumar Ungogo ta Jihar Kano.

Mamatan, wadanda aka fi sani da Almajirai, daliban Tsangayar Malam Iliyasu Mai Tsangaya ne da ke Kadage Sharifai a ƙaramar hukumar Ungogo.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya yi wa APC yasa a Kano, manya a jam'iyyar sun rungumi Kwankwasiyya

Kano.
Taswirar jihar Kano da ke Arewacin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Leadership ta ruwaito cewa Alaramma Sani Musa Nuhu, shugaban Tsangaya Media Network, ne ya bayyana lamarin a wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Kano.

Yadda almajirai 4 suka mutu a Kano

A cewar sanarwar, an garzaya da almajiran su hudu zuwa Asibitin Koyarwa na Aminu Kano domin ba su kulawar lafiya bayan rashin lafiyar da suka yi sakamakon cin abincin da ake zargin ya gurɓata.

Sai dai an ce daliban sun mutu a asibitin a daren Lahadi, 16 ga Agusta, 2026, lamarin da ya tada hankulan jama'a.

Sanarwar ba ta bayyana irin abincin da almajiran suka ci ba ko kuma abin da ake zargin ya jawo gubar.

Haka kuma, ba a bayyana ko wasu daliban da suka ci abincin sun kamu da rashin lafiya ba ko kuma an fara wani bincike kan lamarin.

An yi wa almajiran jana'iza a Kano

Sanarwar ta kara da cewa tuni aka gudanar da sallar jana’izar mamatan bayan samun izinin Dagaci da kuma shigaban caji ofis na jami'an ‘yan sanda na yankin.

Kara karanta wannan

Mutane sun mutu da gine gine 2 suka rufta kan ɗaliban Islamiyya da ma'aikata a Kano

Daga bisani aka birne gawarwakin almajiran huɗun bisa tsari da koyarwar addinin musulunci, kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Almjiraai.
Wasu almajirai suna tsakiyar karatu a makarantarsu ta Tsangaya Hoto: Sa'eed Iliyasu
Source: Getty Images

Wane mataki hukumomi suka dauka?

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, har yanzu ba a fayyace cikakken abin da ya faru da kuma musabbabin zargin gubar abincin ba.

Haka zalika, babu wata sanarwa a hukumance da rundunar yan sandan jihar Kano ta fitar kan lamarin zuwa yanzu, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Gini ya danne daliban Islamiyya

A wani labarin, kun ji cewa mutane biyar, ciki har da ma’aikatan gini huɗu da ɗalibar makarantar Islamiyya, sun mutu sakamakon ruftawar wasu gine-gine a Kano.

Hatsarin farko ya faru ne a Gaida, kusa da gidan mai na Salbas, inda wani ginin da ake ginawa wanda bai kammala ba ya ruguje kan ma’aikata shida, mutun hudu daga ciki suka rasu.

Lmari na biyu ya faru ne bayan kusan mintuna shida a Kurna, a bayan makarantar firamare, inda wani ginin makarantar Islamiyya mai suna Khadija Idris Bala ya ruguje har daliba daya ta rasu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262