An bayyana abinda cire su Buratai zai jawo wa Najeriya

An bayyana abinda cire su Buratai zai jawo wa Najeriya

Boss Mustapha, sakataren gwamnatin tarayya (SGF), ya ce sauya shugabannin rundunonin sojoji na kasa barazana ne ga Najeriya saboda zai haifar da rabuwar kai.

Mustapha ya fadi hakan ne a wurin taron kaddamar da wani littafi da Samuel Salifu, tsohon sakataren kungiyar kiristoci ta kasa (CAN) ya rubuta. An kaddamar da littafin mai suna 'CAN, addini da shugabaci a Najeriya," ranar Talata.

"Ban gamsu cewa korar manyan hafsoshin soji da ke jagorantar rundunonin sojoji ya dace ba, ba haka kawai ake sallamar mutum daga aiki ba. Akwai ka'idojin da ake bi kafin faruwar hakan, kuma za a yi amfani da ka'idojin idan lokaci ya yi," kamar yadda jaridar Punch ta rawaito Mustapha ya fada.

'Yan Najeriya da dama na cigaba da yin kira ga shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a kan ya sallami shugabannin rundunonin sojoji tare da maye gurbinsu da wasu sabbi.

An bayyana abinda cire su Buratai zai jawo wa Najeriya
Buhari da Boss Mustapha
Asali: Depositphotos

Wasu daga cikin masu kiran a sallami su Buratai na kafa hujja da cewa sun gaza wajen kawo karshen aiyukan ta'addanci na kungiyar Boko Haram a yankin arewa maso gabas, musamman jihar Borno da makwabciyarta, jihar Yobe.

DUBA WANNAN: An kashe sojoji biyu, sojoji sun kone gidaje fiye da 150 a Jos

A daya bangaren, wasu na ganin cewa ya dace shugaba Buhari ya sallami su Buratai ne saboda lokacinsu na barin aiki ya cika amma kuma har yanzu basu ritaya ba saboda shugaba Buhari ya ki maye gurbinsu da wasu sabbi, lamarin da ya haddasa cushewar karin matsayi a rundunonin sojoji na kasa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel