Rashin zaman lafiya ya na da alaka da matsalar rashin abin yi - Aliko Dangote

Rashin zaman lafiya ya na da alaka da matsalar rashin abin yi - Aliko Dangote

Shugaban kamfunan Dangote Group a Duniya, Alhaji Aliko Dangote, ya fito ya yi magana game da sha’anin tsaro da rashin aikin yi da ake fama da shi a kasar nan.

Aliko Dangote wanda duk Nahiyar Afrika babu wanda ya kama kafarsa a dukiya, ya bayyana cewa matsalar rashin abin yi ne ya ke kara jawo rashin tsaro a Najeriya.

Attajirin ya ce a na sa hangen, talauci ne ke jawo rashin zaman lafiya. Haka zalika rashin tsaro ya kan kara kawo matsin lambar talauci a duk inda aka yi rashin dace.

Dangote ya yi wannan magana ne a jiya Ranar Laraba,11 ga Watan Fubrairun 2020, a Garin Abuja, lokacin da ya zanta da wasu ‘Yan gidan Jaridar NTA Star Times.

Wakilan gidan Talabijin na NTA StarTimes na wani shiri mai suna ‘Farmers Reality' a karkashin shugabansu, Chigbo Okoli ne su ka yi hira da fitaccen ‘Dan kasuwar.

KU KARANTA: Forbes: Aliko Dangote ya fi kowa dukiya a Nahiyar Afrika

Rashin tsaro ya na da alaka da matsalar rashin abin yi - Aliko Dangote
Alhaji Aliko Dangote ya ce ya zama dole a yaki rashin aikin yi
Asali: UGC

"Mu na cikin matsala a yau; rashin aikin yi ya yi kamari, babu shakka idan ba mu yi wani abu wajen canza yadda abubuwa su ke tafiya ba, hakan ya na da wani tasiri.”

Alhaji Dangote ya fadawa Dr. Chigbo Okoli cewa idan har lamura ba za su sake zani ba, to daukacin jama’ar Najeriya za su samu kansu a cikin mummunan hali.

“Mun yi amanna cewa rashin tsaro ya na da alaka kai tsaye da talauci. Idan aka samu talauci, to babu mamaki rashin zaman lafiya ya biyo baya.” Inji Aliko Dangote.

“Idan babu zama lafiya, sai talauci ya kara kamari. Don haka dole mu magance wannan matsala. Kuma ina mai tabbatar maka da cewa kowa ya na da rawar da zai taka.”

Wani babban jami’in da ke kula da sadarwa da hulda da sauran masu ruwa da tsaki a kamfanin, Mansur Ahmed, shi ne ya wakilci Dangote a wajen wannan hira jiya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel