NYC: Shugaba Buhari ya ajiye mulki tun kafin Najeriya ta zama kamar Somaliya

NYC: Shugaba Buhari ya ajiye mulki tun kafin Najeriya ta zama kamar Somaliya

Taron kungiyoyin Arewa a karkashin lemar NYSC sun fadawa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a dalilin rashin tsaro da ake ta fama da shi yayin da ya ke ofis.

NYC ta koka game da kashe-kashen da ake yi a halin yanzu a Najeriya, wannan ya sa kungiyar ta ce lokaci ya yi da shugaba Buhari zai tattara kayansa ya bar kujerar mulki.

A cewar kungiyar NYC ta bakin shugabanta na kasa, Muhammad Ishaq, zai fi dacewa da Muhammadu Buhari ya yi murabus kafin Najeriya ta zama irin Somaliya.

Mista Muhammad Ishaq ya yi wannan jawabi ne a birnin tarayya Abuja, ya na mai cewa kasar ta koma halin da ta shiga ciki a lokacin da Goodluck Jonathan ya ke mulki.

Da ya ke magana a Ranar Laraba, Ishaq ya bayyana cewa sha’anin tsaro ya tabarbare, kuma a kan hakan ne ma aka yi waje da gwamnatin baya ta jam’iyyar PDP da ta shude.

KU KARANTA: Ina mamakin yadda har yanzu ake fama da Boko Haram - Buhari

NYC: Shugaba Buhari ya ajiye mulki tun kafin Najeriya ta zama kamar Somaliya
Kungiya ta ce Najeriya na neman zama irin kasar Somalia
Asali: Facebook

Kungiyar ta nuna cewa shugaban kasa Buhari ya gaza cika alkawarin da ya yi wa 'Yan Najeriya na cewa zai kawo zaman lafiya a fadin kasar idan har aka zabe shi.

Ko dai ace halin da ake ciki ya fi na lokacin Jonathan tabarbarewa ko kuma ace akalla abin ya kai irin abin da ya auku a lokacin gwamnatin shugaba Goodluck Jonathan.

Ganin kura ta kai bango a halin yanzu, Mista Ishaq ya ce: Lokaci ya yi da ba za a iya cigaba da daukar wani uzuri ba. “Buhari ya gaza kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

NYC ta kare jawabin ta da cewa: “Watakila bai da niyyar yin haka ne, ko kuma ba zai iyan ba, don haka ya yi murabus, ya ceci kasar nan daga wargajewa gaba daya.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel