Jami’an tsaro yi ram da Shugaban Miyagu a Legas da Masu garkuwa da mutane a Yobe

Jami’an tsaro yi ram da Shugaban Miyagu a Legas da Masu garkuwa da mutane a Yobe

Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya sun kama wasu mutane biyu a karamar hukumar Fika da ke jihar Yobe, da ake zargin cewa masu garkuwa da mutane ne.

Kamar yadda mu ka samu rahoto daga Jaridar Daily Trust, Jami’an tsaro sun kama wadannan mutane ne a lokacin da su ke kokarin karbar kudin fansa.

Jaridar ta ce wadanda ake zargin sun shiga ragar ‘Yan Sanda ne yayin da su ke yunkurin karbar kudi N500, 000 daga Iyalin wasu da su ka yi wa ta’adi.

Kakakin ‘Yan Sandan jihar Yobe, ASP Dungus Abdulkarim, ya tabbatar da wannan samame na Dakarun, ya ce ana kokarin cafke wadanda su ka tsere.

Idan mu ka koma Legas kuma za mu samu labari cewa wasu Dakarun ‘Yan Sanda na musamman, sun cafke wani kasurgumin Mai laifi da ake ta nema.

KU KARANTA: Sarkin Musulmi ya koka da halin rashin tsaro a Najeriya

Jami’an tsaro yi ram da Shugaban Miyagu a Legas da Masu garkuwa da mutane a Yobe
Sufeta Janar na 'Yan Sandan Najeriya, Muhammad A. Adamu
Asali: UGC

‘Yan Sandan Legas sun kama Sikiru Samuel wanda aka fi sani da Samora. Ana zargin cewa wannan Matashi ne ya addabi Yankin Imota a Ikorodu.

Samora Mai shekara 24, shi ne shugaban wata kungiyar ‘Yan daba da ake kira Aiye Confraternity. An kama shi ne tare da wasu Yaransa 8 a cikin Ikorodu.

Kakakin ‘Yan Sandan Legas, Bala El-Kana ya bayyana sunayen sauran wadanda aka kama: Adegboyega Ismaila, Sunkanmi Shonubi, da Adigun Faruq.

Sauran wadanda su ka shiga hannun ‘Yan Sandan sun hada da: Rilwan Akinwale, Victor Uju, Juwon Idowu, Rasak Adebola, sai kuma Kehinde Keshinro.

Jaridar ta bayyana cewa an damke wadannan ‘Yan daba ne kwanaki kadan da kama wasu ‘Yan kungiyar Berry Boys da shugabansu mai suna Mailiki Bello.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel