Miyagu sun hallaka Bayin Allah fiye da 20 a karamar hukumar Giwa

Miyagu sun hallaka Bayin Allah fiye da 20 a karamar hukumar Giwa

Mun samu labari cewa kwanan nan wasu ‘Yan bindiga sun kai hari a Kauyen Bakali da ke cikin Yankin Fatika, a karamar hukumar Giwa, jihar Kaduna.

‘Yan bindiga sun aukawa wannan Kauye na Bakali da ke Arewacin jihar Kaduna ne a Ranar Talata, 11 ga Watan Fubrairu, inda su ka kashe jama’a.

Labari ya zo mana cewa akalla mutane 21 su ka bukunci lahira a sakamakon hari. Daga ciki har da mutane 13 da su ka fito daga cikin wani gida daya.

Malam Sani Bakali wanda ya rasa ‘yanuwa fiye da goma ya shaidawa ‘Yan jarida cewa Miyagun sun shafe sama da sa’o’i biyu su na ta’adi a Kauyen.

“’Yanuwana goma sha daya a kashe a gida. Sun kunshi mata uku da kuma maza takwas duk ‘Ya ‘yan kani na. An rufe su ne a gida, aka babbakesu.”

KU KARANTA: Buhari zai biya diyyar wadanda aka kashe a Auno

Miyagu sun hallaka Bayin Allah fiye da 20 a karamar hukumar Giwa
Wasu ‘Yan bindiga sun kai mummunan hari a Kauyen Jihar Kaduna
Asali: Twitter

‘Yan bindigan sun kashe wasu ‘Yanuwa na biyu a wani gidan. Mun tsinci gawar mutane hudu da aka babbaka yadda ba za a iya gane su ba.” Inji sa.

Mutane 21 ‘Yan bindigan su ka kashe, yayin da ake cigiyar mutane tara yanzu. Sani Bakali ya ce wadannan mutane sun rika buda wuta ne ta ko ina.

A sakamakon wannan mummunan hari da aka kai, an kashe wasu Malaman addini, da kuma Abokai da kuma makwabtan Sani Bakali a wannan Kauye.

“Mun idar da yi wa mamatan 21 sallah kenan, sai ‘Yan bindigan su ka duro Kauyen a kan babura da kimanin karfe 4:00pm su ka shiga harbin jama’a.”

“Mun bizne mutane 20 ne da farko, amma daga baya mu ka samu gawar wani a daji, shi ma mu ka bizne shi.” ‘Yan Sanda sun ce sun tura Dakaru.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel