Amurka ta taimaka mana mu ga karshen Boko Haram - Gbajabiamilla
A cikin makon nan ne shugaban majalisar wakilan tarayya na Najeriya, Rt. Hon. Femi Gbajabimila, ya mika kokon bararsa gaban gwamnatin kasar Amurka.
Femi Gbajabimila ya bukaci kasar Amurka ta taimakawa Najeriya wajen kawo karshen masu tada kafar baya tare da kawo karshen matsalar tsaron da ke damun kasar.
Kakakin majalisar ya yi wannan bayani ne yayin da ya karbi bakuncin Jakadan Amurka a Najeriya, Mary Leonard. Gbajabiamilla ya bukaci jin kokarin da ake yi.
“Me kasar Amurka ta ke yi na taimakawa Najeriya wajen yakar masu tada zaune-tsaye? Ko tsarin dokar Leahy na cinikin makamai ya na kawowa alakarmu cikas?”
Mai girma Gbajabiamilla ya kara da tambayar Mary Leonard inda aka kwana game da wani ciniki da aka yi. “Ina ake ciki a kan batun jiragen Tucano da mu ka saya?
KU KARANTA: Sule Lamido ya caccaki Buhari game da matsalar tsaro
“Majalisa da kuma ‘Yan Najeriya su na damuwa da halin rashin tsaron da ake ciki a Najeriya, kuma ‘Yan kasar da-dama su na sa ran Amurka ta bada gudumuwa.”
Bayan haka, Femi Gbajabiamilla ya yabawa gwamnatin kasar Amurka na dawowa Najeriya Dala miliyan 300 da Marigayi Sani Abacha ya sace daga asusun Najeriya.
A na ta jawabin, Leonard, ta bayyana cewa Amurka a shirya ta ke da taimakawa Najeriya wajen ganin an kawo karshen matsalar rashin tsaron da ake fama da shi.
Bugu da kari, Jakadar kasar Amurkan ta yi alkawari cewa za ta dage wajen ganin an kawowa Najeriya jiragen yakin Tucano da ta saya ba tare da bata lokaci ba.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng