Majalisa ta na so Shugaban kasa ya tsige Hafsun Soji, ya kafa dokar ta baci

Majalisa ta na so Shugaban kasa ya tsige Hafsun Soji, ya kafa dokar ta baci

Majalisar wakilan tarayyar Najeriya ta dawo da maganar sauke hafsun sojojin kasar, bayan ‘Yan ta’addan Boko Haram sun yi ta’adi kwanan nan a Garin Auno, jihar Borno.

A wani zama da aka yi a jiya Laraba, ‘Yan majalisa sun bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sa dokar ta-baci a fadin kasar nan, bayan an sauke manyan sojoji.

Hakan ya biyo bayan maganar da Honarabul Mohammed Tahir Monguno ya mike ya yi a gaban majalisar da taken ‘Sababbin hare-haren Boko Haram a Kauyen Auno.”

Yayin da Femi Gbajabiamilla ke jagorantar zaman, ‘Dan majalisar na Borno ya jagoranci muhawarar da aka tafka a game da danyen harin da aka kai kwanan nan.

“Mu da labari cewa a Ranar Lahadi, 9 ga Watan Fubrairun 2020, an tsare daruruwan Matafiya a hanyar Damaturu zuwa Maiduguri bayan Sojoji sun tafi sun kyale su.”

KU KARANTA: Buhari ya yi murabus kafin Najeriya ta zama wata Somaliya

Majalisa ta na so Shugaban kasa ya tsige Hafsun Soji, ya kafa dokar ta baci
Janar Tukur Buratai ya ce tsige Hafsun Sojoji ba shi ba ne mafita
Asali: Facebook

“An bar daruruwa sun yi carko-carko a Auno. Su na kokarin shafe dare a kan hanya kenan sai ‘Yan Boko Haram su ka auko masu, su ka sace wasu, su ka kona wasu.”

Monguno ya bayyana cewa an sace wasu muane da ke cikin manyan motocin bas biyu, da kuma wata mota kirar Sharon. Sannan kuma an kona motoci 18 da mutane 30.

Daga cikin wadanda aka kona har da karamin yaro. Babu wani babban sansani na Sojoji a kan hanyar Maiduguri-Damaturu, wannan ya sa aka yi garkuwa da mutane.

Honarabul Ndudi Elumelu ya yi tir da yadda Sojoji su ke kyale Matafiya cikin dare a kan hanya. ‘Dan majalisar na PDP ya ce ya kamata lallai a tsige Hafsun Sojojin kasar.

A karshe majalisa ta bada umarni cewa a daina tare Matafiya a kan titi ko da karfe 6:00 ta yi. An bukaci kwamitoci su binciki yadda wannan mummunan hari ya faru.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel