Gwamnan Borno ya yi ma Sojojin Najeriya kaca kaca bayan harin Boko haram a Auno

Gwamnan Borno ya yi ma Sojojin Najeriya kaca kaca bayan harin Boko haram a Auno

Gwamnan jahar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya bayyana bacin ransa bisa yadda Sojoji suke aiki a jahar Borno, har ma ya daka ma babban kwamandan yaki da Boko Haram tsawa saboda yadda suke cutar da jama’a a jahar.

Jaridar The Cables ta ruwaito gwamnan ya nuna bacin ransa ne a ranar Litinin, 10 ga watan Feburairu yayin ziyarar gani da ido da ya kai garin Auno na jahar Borno inda mayakan Boko Haram suka kai farmaki suka kashe mutane fiye da 30.

KU KARANTA: Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da fasinjoji 9 a kan hanyar Abuja

A yayin ziyarar, Zulum ya zargi Sojoji da barin mutane a hannun Boko Haram, inda yace Sojojin daya kamata su samar da tsaro a Auno, amma sai ka ga sun yi tafiyarsu da an ce karfe 5 na yamma ta yi.

Boko Haram sun kai harin ne bayan Sojoji sun rufe hanyar shiga garin Maiduguri daga karfe 5 na yamma kamar yadda dokar ta baci ta tanada, hakan yasa suka datse jama’a da dama a waje, wadannan jama’an ne Boko Haram ta kai ma farmaki ta karkashesu, sa’annan ta kona motocinsu.

Da yake yi ma kwamandan Operation Lafiya Dole bayani, Sunday Igbinomwanhia a inda lamarin ya auku a ranar Litinin, Zulum yace: “Dole ne mu fito fili mu fada muku gaskiya, tunda na zama gwamna Boko Haram sun kai hari Auno sau 6, kuma Sojoji sun fice daga garin Auno.

“Ba wai na raina aikin Sojoji bane, amma mun sha muku magana a kan cewa ya kamata ku kafa sansani a Auno, amma sai ku shiga garin, da zarar an ce 5 ta yi sai ku rufe kofa ta kulle mutane a waje, ku kuma ku koma Maiduguri, wannan bai kamata ba.” Gwamnan ya fada yana daga murya cikin fushi, yayin da jama’a ke masa tafi.

Shi kuma a jawabinsa, babban kwamandan ya bayyana cewa a shirye suke su kare rayukan jama’a da dukiyarsu a jahar Borno, amma yace Sojoji suna can suna fatattakar wasu yan Boko Haram ne a lokacin da aka kai wannan hari.

Kwamandan yace babu yadda za’a yi Sojoji su bari yan ta’adda su karkashe mutane suna ji suna gani, don haka ya yi kira ga jama’a dasu taimaka ma Soji da bayanan sirri domin su basu tsaron daya kamata.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel