Boko Haram: Dakarun Sojin sama sun yi luguden wuta a Yagayaga

Boko Haram: Dakarun Sojin sama sun yi luguden wuta a Yagayaga

Mun samu labari cewa Dakarun Sojojin Operation Rattle Snake III, sun cigaba da bazawa ‘Yan kungiyar ta’addan Boko Haram wuta a wasu yankin jihar Borno.

Sojojin sama sun ci nasarar ganin bayan wasu manyan ‘yan ta’ddan Boko Haram da ke labe a Yankin Alafa Yagayaga, a bangaren Arewa maso Gabashin kasar nan.

Dakarun na Sojin sama sun kai wannan hare-hare ne a Ranar 8 ga Watan Fubrairun 2020, inda su ka yi amfani da jiragen yakin ATF na Sojin Operation LAFIYA DOLE.

Rundunar sun kai wa ‘Yan ta’addan wannan hari ne bayan sun samu labari cewa sun fake a daf da dajin nan na Sambisa domin su gudanar da wani taro da su ka saba.

Bayan Sojojin saman sun tabbatar da isowar ‘Yan ta’addan sai su ka shiga luguden wuta da bama-bamai wanda aka yi dace ya rutsa ‘Yan ta’addan, ya kuma tarwatsa su.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun hallaka wasu mutane a Jihar Kaduna

Boko Haram: Dakarun Sojin sama sun yi luguden wuta a Yagayaga
Shugaban Hafsun Sojojin sama na Najeriya, Air Marshall Abubakar Sadiq
Asali: UGC

Bama-baman da aka saki da jiragen saman a Ranar Asabar sun ruguza sansanin da ‘Yan ta’addan su ke fake, sannan kuma barin wutan ya sa an fatattake su daga yankin.

Rundunar Sojin saman za ta cigaba da kokari na rike wuta da jiragen saman yaki domin ganin an ga karshen ‘Yan ta’addan Boko Haram a Arewa maso Gabashin kasar.

Mai magana da yawun bakin Dakarun sojojin saman Najeriya, Ibikunle Daramola ne ya fitar da wannan bayani a madadin Jami’an tsaro a Ranar 10 ga Watan Fubrairu.

Bayan haka Jami’an sojojin sun fitar da bidiyo a Facebook da aka dauka domin ganin yadda luguden wutan da aka yi daga sama ya yi tasiri a kan ‘Yan Boko Haram.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel