'Yan Bindiga Sama da 100 Sun Tafka Ta'asa yayin Wani Hari a Katsina
- ‘Yan bindiga sun kashe mutane uku tare da jikkata wasu biyar a harin da suka kai Dansarai da ke karamar hukumar Malumfashi ta Katsina
- Maharan sun kuma sace wata mata tare da kwashe dabbobi da ba a tantance adadinsu ba yayin harin da ya dauki kusan sa’o’i biyar
- Wani mazaunin yankin ya ce ana zargin harin ramuwar gayya ne bayan mazauna garin sun dakile wani yunkurin harin 'yan bindiga watanni uku da suka gabata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Katsina - Akalla mutane uku ne aka kashe, yayin da wasu biyar suka samu raunuka, bayan da ‘yan bindiga suka kai hari garin Dansarai da ke karamar hukumar Malumfashi ta jihar Katsina.
Maharan sun kuma yi awon gaba da wata mata tare da satar dabbobi da ba a bayyana adadinsu ba a yayin harin da suka kai garin da misalin karfe 5:00 na yammacin Juma’a, 14 ga watab Agustan 2026.

Source: Facebook
Wani mazaunin yankin, Shafiu Umar, ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa ‘yan bindigar sun iso ne a kan babura kusan 50, inda kowane babur ke dauke da mutane uku dauke da makamai.
'Yan bindiga sun yi ta'asa a Katsina
'Yan bindigan sun shafe kusan shafe sa’o’i biyar suna gudanar da ayyukansu na barna da ta'addanci a kauyen.
Shafiu Umar ya ce maharan sun rika shiga gidaje daya bayan daya, suna kwashe kayayyaki daga shaguna tare da razana mazauna yankin.
A cewarsa, ‘yan bindigar sun kuma kutsa cikin shaguna tare da kwashe wayoyin hannu, kayan abinci, tufafi da sauran kayayyaki masu daraja.
Ana zargin harin na ramuwar gayya ne
Shafiu Umar ya ce ana zargin harin ramuwar gayya ne kan wani lamari da ya faru kimanin watanni uku da suka gabata, lokacin da mazauna garin suka tunkari ‘yan bindiga da suka yi yunkurin mamaye yankin.
“Tun bayan wannan lamarin muke rayuwa cikin tsoro. Wannan sabon harin ya yi kama da ramuwar gayya ne saboda mazauna yankin sun dakile su a wancan lokacin,” in ji shi.
An kashe mazauna garin uku a harin, yayin da wasu biyar suka samu raunukan harbin bindiga. An kuma yi awon gaba da wata mata.
Kauyen Dansarai ya sha fama da hare-hare
Kauyen Dansarai wanda ke gabashin karamar hukumar Malumfashi, yana da iyaka da karamar hukumar Gwarzo ta jihar Kano.
Al’ummar yankin sun sha fuskantar hare-haren ‘yan bindiga a shekarun baya, lamarin da ya yi sanadin kashe-kashe, sace mutane, satar dabbobi da kuma raba wasu mazauna da muhallansu.
Me 'yan sanda suka ce kan lamarin?
Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina, DSP Sadiq Aliyu, ya ce zai tabbatar da bayanan sannan ya dawo da martani.
Sai dai har zuwa lokacin kammala hada wannan rahoto, kakakin 'yan sandan bai sake tuntubar manema labarai ba.

Source: Original
'Yan bindiga sun kashe mutane
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu tarin 'yan bindiga sun kai gagarumin hari jihar Sokoto, inda suka kashe mutane da dama.
'Yan bindigan sun ajiye babura a gaban masallaci kafin su tarwatsa masu ibada sannan suka shiga cikin gari, inda suka kashe mutane.
Asali: Legit.ng

